NDLEA ta kama tabar wiwi da ake shirin fitawa zuwa Amurka da Ingila, / Hoto: shafin X na NDLEA

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta kama tarin miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye a cikin gwangwanin abinci da kayan jarirai waɗanda aka shirya fitar da su zuwa ƙasashen Amurka da Ingila.

Jami'an hukumar sun yi kamen ne a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Murtala Mohammed (MMIA) da kuma na ɗaukar kaya da ke jihar Lagos a kudu maso yammacin Nijeriya, kamar yadda NDLEA ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi.

Hukumar ta ce nauyin ƙwayoyin ya kai kilogram 18.50.

Daga cikin miyagun ƙwayoyin da aka kama, har da ledar tabar wiwi guda 36 da aka ɓoye a cikin kwalin abincin jarirai mai suna Nestle Cerelac - kowanne na da gwangwani guda shida - inda aka gano su a wurin ajiye kayayyaki da ake fitarwa waje na SAHCOL a filin jirgin saman Legas a ranar Labara 31 ga watan Yuli na 2024.

NDLEA ta kama tabar wiwi da ake shirin fitarwa zuwa Amurka da Ingila, / Hoto: shafin X na NDLEA

Kazalika hukumar ta bayyana cewa, ta kama wata jami'ar da ta kawo kayan mai suna Salaudeen Suliat Abiola da aka shirya fitar da su zuwa Ingila, yayin da a wani samame da ta kai jihar Oyo a ranar Asabar, 3 ga watan Agusta ta kama Bello Motunrayo wanda ya aika da kayan.

''An rufe saman gwangwanin abincin jariran kamar dai yadda ake sayarwa daga masana'antar da ke haɗa su, sai dai daga ƙasa akwai alamun an buɗe, inda muka gano an lulluɓe miyagun ƙwayoyin da wani adadi na garin abincin jarirai don gudun kar a gano," in ji sanarwar.

NDLEA ta ƙara da cewa, jami'anta a Legas sun yi nasarar kama wasu miyagun ƙwayoyi waɗanda suka haɗa da promethazine da pentazocine da diazepam da tramadol da kuma morphine da aka ɓoye su a cikin kayan sawa da wasu kayayyaki da ake shirin fitarwa zuwa Amurka da Ingila.

''Ɗaya daga cikin kayan da ake shirin fitarwa zuwa Amurka wanda nauyinsa ya kai giram 820 na ɗauke da ƙwayoyin promethazine da allurar pentazocine, yayin da sauran ƙullin kayayyaki huɗu da aka kama waɗanda ake shirin fitar da su zuwa Ingila suke ɗauke da ƙwayoyin Tramadol da Molly da NPS,'' a cewar NDLEA, inda ta ƙara da cewa gaba ɗaya an kama su ne a ranar Litinin, 29 ga watan Yuli, a wani kamfani da ke birinin Legas.

TRT Afrika