Jami’an Hukumar Yaƙi da Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya NDLEA, sun yi nasarar kama hodar ibilis wadda kuɗinta ya zarta naira biliyan 4.4 a Legas.
A wata sanarwa da hukumar ta NDLEA ta fitar a ranar Lahadi, ta ce jami’an nata sun gano hodar ibilis ɗin a cikin ban-ɗakuna biyu na wani jirgin sama na ƙasar Ethiopia wanda ya taso daga Addis Ababa zuwa Legas.
Hukumar ta NDLEA ta bayyana cewa wani gungun masu safarar ƙwayoyi a tsakanin Brazil da Ethiopia da Nijeriya ne suka yi ƙoƙarin shigar da ɗauri 845 na hodar ibilis ɗin cikin Nijeriya wanda nauyinta ya kai kilo 18.72.
NDLEA ɗin ta bayyana cewa an naɗe hodar ibilis ɗin a cikin ledoji tara inda aka ɓoye su a cikin ban-ɗakuna biyu da ke cikin jirgin, kuma an gano su ne bayan da aka ankarar da jami’an na NDLEA ɗin da ke filin jirgin sama na Legas dangane da abubuwan da aka gani.
Aƙalla mutum 30 hukumar ta NDLEA ɗin ta tsare inda ta yi musu tambayoyi sakamakon faruwar wannan lamari, kamar yadda ta tabbatar.
Ana yawan samun rahotannin safarar miyagun ƙwayoyi a Nijeriya inda akasarinsu ake shigar da su ƙasar daga wasu ƙasashen waje.
Sai dai hukumar ta NDLEA ta sha jaddada cewa tana iya bakin ƙoƙarinta domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyin. Domin kuwa ko a kwanakin baya sai da hukumar ta NDLEA ta kama ƙwayoyi na fiye da naira biliyan 14 a ƙasar.