A kwanakin baya ne NDLEA ta yi gargadi kan amfani da A-kuskura. Hoto/NDLEA

Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyin a Nijeriya, NDLEA, ta ce ta gano wani kamfani da ake hada A-kuskura a garin Mubi na Jihar Adamawa.

Hukumar ta ce kamfanin ya gawurta har yana fitar da A-kuskura zuwa kasashen Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar.

Kakakin hukumar ta NDLEA Femi Babafemi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar mai kunshe da bayanai kan kamen da suka yi na miyagun kwayoyi.

Babafemi ya bayyana cewa a lokacin da da aka kai samamen, ana cikin aikin hada A-kuskura.

A-kuskura wani hadi ne ko kuma jiko da ke sa mutum maye ko kuma ya fita daga cikin hayyacinsa musamman a karon farko da aka soma amfani da shi.

Haka kuma hukumar ta ce ta kai samame a wani kango da ke cikin wani daji a garin Ala da ke yankin Akure a Jihar Ondo inda ta gano akalla buhu bakwai na tabar wiwi.

Baya ga haka kuma akwai dauri 126 na tabar wiwi nau’in ‘Canadian Laud’ cikin mota kirar Corolla da aka yi safararta daga Jihar Toronto ta Canada. An kama wiwin ne a tashar ruwa ta Tincan da ke Legas.

A Jihar Benue kuwa, hukumar ta ce ta kama kwalaben maganin tari na codeine 859 wadanda nauyinsu ya kai kilo 117.3 wadanda ake zargin wani dillalin kwayoyi ne ya jefar da su kimanin kilomita biyu kafin shingen binciken NDLEA da ke hanyar Enugu zuwa Otukpo.

TRT Afrika da abokan hulda