Yawan tsaikon da aka yi ta smau a tafiya a lokacin bikin Kirsitimeti ya sa an samu ƙari da yawa na ƙorafe-ƙorafen matafiya game da jinkiri da kuma soke tafiya.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta hukunta kamfanonin jiragen sama biyar (biyu na ƙasa-da-ƙasa, uku na cikin gida) kan aikata laifuka daban-daban.

Laifukan sun haɗa da rashin mayar da kuɗi a kan lokaci ga matafiyan da ba a yi wa adalci ba da rashin bin umarnin hukumar jiragen da rashin bi da kayan matafiya a hankali da soke tafiye-tafiye da sauransu.

Mai magana da yawun hukumar ta NCAA, Michael Achimugu, shi ya bayyana wa manema labarai wannan labari a babban ofishin hukumar da ke Abuja ranar Talata.

Ya ce ko da yake ba ko wane lokaci ba ne kamfanonin ke aikata laifin soke tafiya, amma dokokin NCAA sun bayyana matakan da suka kamata kamfanonin jirage su ɗauka a lokacin da aka samu tsaiko a tsarin tafiye-tafiye.

Ya ce rashin bin waɗannan matakai na iya sawa a hukunta kamfanonin.

A kwanan baya ne hukumar NCAA ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki mataki idan kamfanonin jiragen saman Nijriya suka ƙi mayar wa fasinjoji kuɗaɗensu cikin kwanaki 14 ga waɗanda suka sayi tikitin jirginsu ta intanet ko kuma nan-take ga tikitin da aka saya da takardar kuɗi.

Yawan tsaikon da aka yi ta samu a tafiye-tafiye a lokacin bikin Kirsitimeti ya sa an samu ƙarin ƙorafe-ƙorafen daga matafiya game da jinkiri da kuma soke tafiya.

“Dukkanmu mun san wannan lokacin hunturu ne, saboda haka akwai hazo sosai mutane ba sa iya gani sosai. Dole a soke tafiyar jirage. Kamfanonin jiragen ba sai sun mayar wa matafiya kuɗaɗensu ba a irin wannna halin. Matakan da muke ɗauka a yau muna ɗaukarsu ne a yanayin da kamfanonin jiragen saman ke da laifi,” a cewar mai magana da yawun hukumar.

Ya bayar da tabbacin cewar hukumarsa za ta kira dukkan shugabannin kamfanonin jiragen sama a wannan makon domin tattaunawa game da tsaikon da suke yi na jigilar jama'a da kuma bijre wa doka.

Achimugu bai bayyana sunayen kamfanonin jiragen da hukumar ta hukunta ba.

TRT Afrika