NAFDAC ta ce amfanin wasu daga cikin kayan da ake sayarwa a kantin ya ƙare amma ba a daina sayar da su ba. . Hoto: NAFDAC X

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya (NAFDAC), ranar Litinin ta rufe wani babban kanti na 'yan China bisa zargin sayar da kaya da aka sanya musu tambari da harshen China ba tare da an tuntuɓi hukumar ba.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN, ya ruwaito cewa kantin yana unguwar Wuse 2 a Abuja, babban birnin ƙasar.

NAN ya ambato Daraktan da ke gudanar da bincike na NAFDAC, Shaba Mohammed, yana shaida wa manema labarai cewa an sanya tambari da harshen China kan galibin kayan da ake sayarwa a kantin, matakin da ya saɓa wa dokokin hukumar.

"Za mu gudanar da bincike kan fiye da kashi 90 na kayan da ke cikin kantin waɗanda aka sanya wa tambarin China tare da gano yadda aka shigo da su ƙasar nan," in ji daraktan.

Shaba Mohammed ya ƙara da cewa amfanin wasu daga cikin kayan da ake sayarwa a kantin ya ƙare amma ba a daina sayar da su ba.

TRT Afrika