Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) ta gargadi ‘yan kasar da su yi taka tsantsan wajen shan wani gurbataccen lemon kwalba na Sprite mai yawan 50cl da ya watsu a kasar.
Hukumar ta sanar da hakan ne a shafinta na Twittewr a ranar Laraba.
“Mun samu korafi ne kan wannan lemo daga wajen masu amfani da shi sannan sashen sa ido kan kayayykin da ake sayarwa na hukumar ya yi bincike a kai,” in ji sanarwar.
Ta kara da cewa, binciken da ta yi a adireshin wanda ya saya da inda ya saya din ya gano kiret biyar na lemon kwalbar duka da wasu gurbatattun sinadarai a cikinsu.
“Tuni aka kai lemon dakin gwaji na NAFDAC don fayyacewa, kuma mun yi kira ga dukkan daraktocin hukumar na shiyyoyin kasar da su yi bincike don gano sauran gurbatattun lemon da watakila suka watsu.”
NAFDAC ta kuma za ta gudanar da cikakken bincike a wajen da ake samar da lemon don gano ta inda ya gurbata.
Sannan tuni aka bai wa kamfanin da yake samar da lemon wato Nigerian Bottling Company Limited da ke Abuja, umarnin janye dukkan lemon daga kasuwa don NAFDAC ta samu damar sa ido sosai.