Ana fargabar adadin zai ƙaru zuwa miliyan 52 nan da tsakiyar baɗi. / Hoto: Reuters Archive

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan 40 ne suke fama wajen ciyar da kansu a faɗin Yammaci da Tsakiyar Afirka.

Ana fargabar adadin zai ƙaru zuwa miliyan 52 nan da tsakiyar baɗi.

Wani sabon rahoton da hukumar ta fitar ranar Juma'a, ya ce a halin da ake ciki mutum miliyan 3.4 suna fuskantar “yunwa matakin ko-ta-kwana” a yankin, wanda ke nufin ƙarin kashi 70 cikin ɗari tun bazarar bana.

Rahoton ya ce rikice-rikice, da ɗaiɗaitar mutane, da rashin daidaituwar tattalin arziƙi, da tsanantar tasirin sauyin yanayi suna janyo rashin wadatar abinci.

Rikicin da ake a yankin Sahel, da kuma yaƙin basasan Sudan, sun tilasta ɗaiɗaitar sama da mutane miliyan 10 a faɗn yankin.

Gagarumar ambaliya a Nijeriya da Chadi a wannan shekarar ya ƙara azanta lamarin.

Matsalar yunwa mai maimaituwa

Duk da adadin yana da ban-tsoro, sabon rahoton ya rage ƙiyasin bara na yawan mutanen da ke fuskantar rashin wadatar abinci da mutane miliya 7.7.

Hukumar WFP ta ta'allaƙa raguwar adadin kan ƙaruwar wadatar ruwan sama da kyautatuwar tsaro, wanda babu tabbacin ya ci gaba da kyautatuwa.

Duk da haka, rahoton na WFP ya ce a shekara mai zuwa, rashin wadatar abinci zai shafi duk mutum guda cikin mutane goma a Yammaci da Tsakiyar Afirka, wanda bankin Duniya ya ƙiyasta yana da al'ummar da ta kai rabin biliyan.

Daraktan WFP na yankin Yammacin Afirka, Margot van der Velden ya ce “matslar yunwa mai maimaituwa” a yankin za ta kau ne ta hanyar kyautata tsari da shiri.

Van der Velden ya ce, “Muna buƙatar samar da kuɗi kan-lokaci, yadda ake buƙata don cim ma mutane don ba su tallafi, da zuba kuɗi kan ayyukan shiryawa bala'i, don shiryawa don ƙarfafa al'ummomi masu buƙatar jin-ƙai”.

TRT World