Wani gini mai hawa shida da ake tsaka da ginawa ya ruguje a babban birnin kasuwanci na kasar Ivory Coast, Abidjan.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a inda akalla mutum bakwai suka rasu, kamar yadda masu kashe gobara da ke wurin suka bayyana.
Ma’aikatan sun bayyana cewa suna cikin aiki da tsakar rana sai suka soma jin karar gini na tsagewa, inda ya ruguzo a kansu, kamar yadda mai kula da aikin ginin Jourdin Yoro ya shaida.
“A cikin sauri, sai muka soma gudu,” kamar yadda Yoro ya bayyana. “Cikin kusan dakikoki 45, sai ginin ya ruguje.”
Ana ci gaba da kokarin ceto mutane a gundumar Riviéra Palmeraie da ke Abidjan inda masu aikin ceto ke ta duba baraguzai domin ceto jama’a.
Karin mutum tara sun samu rauni a lokacin da ginin ya fado, kamar yadda Charles Paolo, shugaban ma’aikatan kashe gobara ya bayyana.
Ana yawan samun rushewar gini a Ivory Coast da kuma wasu sassa na Yammacin Afirka musamman a lokacin damina sakamakon karancin bin ka’idoji wurin gine-gine da kuma yawan amfani da kayayyaki marasa inganci.
A 2022, gwamnatin Ivory Coast ta bayyana cewa za ta kara kaimi wurin tabbatar da cewa ana bin ka’idojin gini bayan gine-gine biyu da suka da suka ruguzo har suka yi sanadin mutuwar mutum 13.
Duka gine-ginen sun ruguzo ne a lokuta daban-daban amma a cikin makonni biyu.