A 'yan kwanakin nan, an yi ta gudanar da zanga-zangar kokawa kan tsadar rayuwa a Nijeriya. / Hoto: Vanguard newspaper

Wasu mutane sun yi wawason kayan abinci daga wani rumbun gwamnati da ke birnin tarayya Abuja ranar Lahadi.

Josephine Adeh, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Abuja, ta tabbatar da faruwar lamarin, ko da yake ta ce an "shawo kan" lamarin.

A safiyar Lahadi ne mutane suka kai hari kan ma'ajiyar da ke unguwar Karimo a yankin Abuja Phase 3.

Jami'an 'yan sanda da aka jibge a ma'ajiyar sun samu nasarar korar dandazon mutanen a cewar Adeh. Rundunar 'yan sandan ta ce ta kama mutum 15 da ake zargi da hannun a wawason kayan abincin.

Zanga-zanga

Nijeriya ta fuskanci yawaitar zanga-zanga kan tsadar rayuwa, inda fusatattun mutane ke zargin shugaban ƙasa Bola Tinubu da aiwatar da matakan da ke ƙuntata wa 'yan kasa, da suka haɗa da cire tallafin man fetur.

Shugaban ya amsa cewa yana sane da matsin rayuwar da ke addabar 'yan Nijeriya, amma ya bayyana kyakkyawan fatansa kan ganin shirye-shiryen gwamnatinsa sun haifar da ɗa mai ido, inda ya ce tattalin arziƙin ƙasar zai inganta.

TRT Afrika