Rahotanni daga Abuja, babban birnin Nijeriya na cewa mutane da dama sun mutu sakamakon ruftawar wani gini yayin da ake shatata ruwan sama ranar Laraba da daddare.
Lamarin ya faru ne a unguwar Garki da ke tsakiyar birnin, kamar yadda gidan talabijin na kasa, NTA, ya rawaito ko da yake ya ce mutum biyu ne suka mutu ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin.
Ya kara da cewa mutum talatin da bakwai ne suka jikkata.
Sai dai bidiyoyin da aka rika watsawa a shafukan intanet sun nuna yadda mutane suke fitar da kaya daga baraguzan ginin.
Jaridar Punch da ake wallafawa a kasar ta ce ginin, mai fiye da hawa daya, yana cike da mutane a lokacin da ya rufta.
Kazalika ta ambato wasu ganau suna cewa mutane da dama ne suke zaune a ginin yayin da wasu suka yi hayar dakunan da ke kasa domin yin kasuwanci.
Kawo yanzu dai hukumomin bayar da agaji irin su FCT Emergency Management Agency, FEMA, da hukumar kashe gobara da hukumar kiyaye hadura suna ci gaba da aikin ceton mutanen da suka makale a cikin ginin.
Har yanzu babu cikakken bayani game da abin da ya haddasa ruftawar ginin.
Nijeriya ta dade tana fama da matsalar rushewar gine-gine wadda ake dangantawa da rashin bin ka'idojin gini.