A ranar Laraba ne wata kotu a kasar Guinea ta yanke wa tsohon shugaban mulkin sojan kasar Moussa "Dadis" Camara hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari, bayan da ta same shi da laifin cin zarafin bil'adama a kisan kiyashin da sojoji suka yi a filin wasa a shekarar 2009 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 157 tare da yi wa mata da dama fyade.
Kotun hukunta manyan laifuka ta Guinea ta yanke wa Camara da wasu manyan jami'ai bakwai hukunci bayan shafe tsawon lokaci ana shari'a kan laifukan kisan kai da garkuwa da mutane da fyaɗe, waɗanda aka mayar da su a matsayin "laifi na cin zarafin bil'adama" a ranar Laraba.
An wanke sauran mutum huɗun da ake zargin su a aikata laifin.
Fiye da mutane 100 da suka tsira da ’yan'uwan wadanda abin ya shafa sun ba da shaida a shari’ar da aka fara a watan Nuwamba 2022, fiye da shekaru goma bayan kisan kiyashin da kuma matsin lamba daga iyalai da masu fafutuka na neman a yi musu adalci.
'Wasu da aka kasa iko da su'
Masu zanga-zangar a filin wasan a watan Satumbar 2009 suna nuna adawa da shirin Camara na tsayawa takarar shugaban kasa lokacin da sojoji suka bude musu wuta tare da yi wa mata da dama fyade. Shugaban sojojin na wancan lokacin ya yi juyin mulki a shekarar da ta gabata.
Gwamnatin mulkin sojan a lokacin ta ce ‘yan bindigar da aka kasa iko da su ne suka aikata fyade da kashe-kashe. Sai dai manyan mataimakan Camara sun kasance a filin wasan, kuma ba su yi wani abu ba don hana kisan kiyashin, in ji rahoton Human Rights Watch.
Yawancin wadanda aka kashe a zanga-zangar filin wasan, an harbe su, ko murkushe su ko kuma aka kashe su da wuka har lahira yayin da wasu daga cikin matan kuma aka fitar da su daga inda suke ɓoye inda gungun mutane suka yi musu fyade a tsawon kwanaki da dama, kamar yadda shaidu suka bayyana.
Wasu da dama sun kasa tsere wa harbin bindigar bayan da jami'an tsaron Shugaba Camara suka kewaye filin wasan tare da toshe hanyoyin fita, in ji wadanda suka tsira.
'Ina barci'
An dauki kwanaki da yawa kafin a bar iyalan wadanda lamarin ya shafa su zo su kwashe gawarwakin, a cewarsu yayin shari’ar. Mutane da yawa, duk da haka, ba su sami gawar 'yan'uwansu ba.
Camara ya tsere zuwa gudun hijira bayan ya tsallake rijiya da baya bayan wani yunkurin kashe shi da aka yi watanni da dama bayan kisan kiyashin amma ya koma Guinea fiye da shekaru goma bayan haka.
“Idan na zo gabanku saboda kishin kasata ne, in ba haka ba da ban yarda in zo ba,” in ji shi a ranar farko a gaban kotu da zai fuskanci shari’a a shekarar 2022, inda ya kara da cewa yana barci ne a lokacin da aka yi kisan kiyashi.
Yayin da yake gidan yari a karshen shekarar da ta gabata, wasu ‘yan bindiga sun sako Camara, wadanda suka kai hari babban gidan yarin kasar, amma bayan sa’o’i an mayar da shi gidan yarin, lauyansa ya ce an yi garkuwa da shi ne.