Kamfanin Meta ya ce ya cire wasu shafukan Facebook kusan 63,000 a Nijeriya da suka yi yunƙurin zambatar maza da dama a Amurka.
'Yan damfarar na intanet a Najeriya, wadanda aka fi sani da "Yahoo boys", sun yi ƙaurin suna wajen zamba da suka haɗa da nuna kansu a matsayin masu bukatar kudi ko su ce su 'ya'yan sarakuna ne a Nijeriya, inda suke yi wa wadanda suke hilata alkawarin samun gagarumar riba idan Amurkawan suka zuba jari.
Meta ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa shafukan da aka cire sun kuma hada da wata ƙaramar ƙungiya mai mutum kusan 2,500 wadanda ke da alaƙa da gungun mutum kusan 20.
Meta ya ce "Sun fi haƙon maza ne a Amurka kuma suna yin amfani da shafukan ƙarya don yin ɓad-da-kama.
Bayan cin tarar Meta da Nijeriya ta yi
Binciken ya nuna cewa yawancin yunƙurin ƴan damfarar bai yi nasara ba kuma ko da yake galibi maza manya ake haƙo, to an kuma yi yunƙurin yi wa yara ƙanana, wanda Meta ya ba da rahoto ga Cibiyar Kula da Yaran da suka Ɓata ta Ƙasa a Amurka.
Sanarwar da Meta ta fitar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Nijeriya ta ci tarar kamfanin dala miliyan 220 bayan bincike ya nuna cewa bayanan da ake watsawa a shafukan sada zumuntar ya saɓa wa dokar kariyar bayanan jama’a.
Hukumar da ke bai wa kowa damar saka haja a kasuwa da kuma kare muradun masu sayayya ta Nijeriya (FCCPC) ta ce Meta ta tattara bayanan masu amfani da shafukanta a Nijeriya ba tare da izininsu ba, ta hanyar wuce gona da iri a harkokinta da kuma ƙin kare bayanan sirrin masu amfani da shafukan, kuma ta ci gaba da nuna wariya da nuna bambanci ga 'yan Nijeriya.
A yayin ya rufe dubban shafukan a Nijeriya, Meta ya ce ya yi amfani ne da hadakar sabbin alamu na fasaha da aka ƙirƙira don taimakawa wajen gano masu tatsar mutane kuɗaɗe.
'Yan 419
An fi kiran 'yan damfara a Nijeriya da suna “'yan 419” wato sunan sashen dokar hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ya yi aiki – ba tare da wani tasiri ba – don magance zamba.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, yayin da yanayin tattalin arziki ke ƙara taɓarɓarewa a kasar mai mutum sama da miliyan 200, zamba ta intanet ta ƙaru, inda wadanda ke aikata hakan kan gudanar da ayyukansu ko da daga dakunan kwanansu a jami’o’i ko da unguwannin marasa galihu ko kuma unguwannin masu wadata.
Meta ya ce wasu shafukan kuma suna ba da shawarwari kan yadda za a gudanar da zamba.
"Kokarin da suka yi ya hada da bayar da sayar da rubuce-rubuce da matakan da za a yi amfani da su yayin damfarar mutane, da kuma musayar hanyoyin tattara hotuna da za a yi amfani da su wajen inganta asusun ƙarya," in ji ta.