Ƙarfin sojin Maroko a fagen yaƙi a teku ya samu haɓaka bayan sabon cinikin makami mai linzami mai suna “fire-and-forget”, sama da 600 daga Amurka.
A wata sanarwa ta baya-bayannan nan, Hukumar Haɗin-kan Tsaro ta Defense Security Cooperation Agency (DSCA), ta sanar da sayar da makamai na kimanin dala miliyan $260 ga ƙasar da ke Arewacin Afirka.
Sanarwar ta DSCA ta ce, “Gwamnatin Maroko ta nemi siyan makami mai linzami na Javelin FGM-148F guda 612, wanda ya haɗa da makamai masu linzami na fly-to-buy guda 12, da kuma makamin Javelin Lightweight Command Launch Units (LWCLUs) guda 200”.
Makami mai linzami na Javelin, makami ne mai matuƙar ƙarfi wajen tarwatsa tankar yaƙi, da dakarun soji ke amfani da shi a faɗin duniya, a cewar kamfanin Amurka na Lockheed Martin.
Makaman suna da sauƙin ɗauka kuma mutum ɗaya na iya sarrafa su. Hakan na nufin dakaru suna iya daidaita makamin daga kan kafaɗunsu.
Makamin mai linzami da aka fi sani da “fire-and-forget”, ba ya buƙatar mai sarrafa shi ya jagorance shi wajen kai wa ga abin da aka hara.
Maimakon haka, makamin yana bibiyar abin da zai hara yayin da yake cikin iska, sannan ya sake saita hanyarsa don tabbatar da cimma harin. Wannan yana ba da dama ga dakaru su sake loda makamin don kai wani harin.
Amma wani fitaccen aikin makami mai linzami na Javelin shi ne iya kai hari ta sama, inda yake harar ɓangaren mota da ya fi rashin kauri, wato rufin samanta.
Wannan cinikin makamai na Amurka ya haɗa da jerin tallafin kayan aiki, da na horo, kan makamin, wanda zai ƙunshi ziyarar jami'an Amurka duk shekara zuwa Maroko tsawon shekaru bakwai.
Cinikin na zuwa ne yayin da takun-saƙa tsakanin Maroko da maƙwabciyarta Algeria ke ƙaruwa, game da saɓani kan Western Sahara, wanda Maroko ke iƙirarin cewa yankinta ne, amma Algeria take goyon bayan 'yan tawayen Polisario Front da ke fafutuka a yankin.
To, ko wannan cinikin makamai daga Amurka zai haɓaka yunƙurin Maroko na neman wannan yanki?
Ciniki da Amurka
Ba wannan ne karo na farko da Maroko ta sayi tarin makaman soji daga Amurka ba.
A zahiri ma, Amurka da Maroko sun ci gaba da daɗaɗɗen haɗin-gwiwa a ɓangaren soji, wanda ya haɗa da atisayen haɗin-gwiwa, da ayyukan ba da horo da musayar jami'ai.
A Afrilun bara, Ma'aikatar Harkokin Waje ta Amurka ta amince da sayar da makamai na kusan dala miliyan $750 ga Maroko. Wannan ya haɗa da shirin haɗin-gwiwa na Joint Stand Off Weapons (JSOW), da kuma shirin HIMARS na makaman ATACMS.
A lokacin, masu sharhi sun saɓa a ra'ayinsu game da cinikin. Wasu sun ce, hakan ya “nuna yadda ƙasar ta Afirka ke ƙoƙarin zamanantar da kanta”.
David Des Roches, wani farfesa a Cibiyar Nazarin Tsaro ta Near East South Asia Center, ya faɗa wa Breaking Defense cewa wannan cinikin na makamai bai ba da mamaki ba.
Roshes ya ce, “Sojin Maroko suna cikin mafi ƙwarewa a duniya kuma sun fi karkata ga ra'ayoyin ƙasashen Yamma".
Sai dai kuma, wasu masana sun koka kan tashin-tashina a yankin yayin da Maroko ke ci gaba da haɓaka ƙarfin sojinta.
A kasafin 2024-2025, gwamnatin Maroko ta ƙara kuɗaɗen da take kashewa don “sayowa da kula da kayan aiki na dakarun sojinta, da tallafawa gina masana'antarta ta tsaro” da kashi 4.1% cikin ɗari, cewar rahoto daga Agencia EFE.
An ruwaito cewa wannan adadin da aka ware ya kai Euro biliyan 11.3, wanda shi ne kaso 9.6% cikin ɗari na GDP ɗin kasar.
A ɓangarenta, Amurka na kallon wannan ciniki da Maroko a matsayin tallafi kan manufofinta na ƙasashen waje, da kare muradunta na tsaron ƙasa.
Sanarwar ta DSCA ta yi nuni da cewa a matsayin Maroko na ƙawarta wadda ba ta cikin NATO, kuma wata babbar madogara game da ɗorewar zaman lafiya a Arewacin Afirka, kuma ta yi iƙirarin cewar cinikin baya-bayan nan “ba zai sauya daidaiton ƙarfin soji a yankin ba”.
Gabanin faruwar wannan, dole sai Majalisar Dokokin Amurka ta amince da duk Wani Cinikin Kayayyakin Soji da Ƙasashen Waje, kuma suna iya sauyawa idan farashi ko adadi ya sauya lokacin tattaunawa.
Don haka muna jira mu gani idan cinikin zai tafi a haka, sannan ko hakan ba zai canja daidaiton ƙarfin soji a yankin ba.