Matatar man Dangote ta ce ta cim ma wata gagarumar nasara inda ta sayar wa kamfanin man Saudiyya (Saudi Aramco) man jiragen sama.
Matatar ta Dangote ta ce tuni ta aika da jiragen ruwa biyu dauke da man zuwa Saudiyya.
Saudi Aramco shi ne kamfanin man Saudiyya wanda kamfani ne na man fetur da kuma iskar gas.
Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote, shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin da Ma’aikatan Cibiyar Nazarin Tattalin Arziƙin Nijeriya, wato Nigerian Economic Summit Group (NESG) suka kai ziyara kamfanin takin Dangote da kuma matatar man Dangote da ke Legas.
Dangote ya ce fitar da man zuwa kasuwar duniya, musamman ga Saudi Aramco, ya faru ne saboda ingancin matatar da kuma ingancin fasahar kayayyakin aikin ta.
“Mun kama hanyar cim ma burin da muka saka a gaba, kuma na yi murnar bayyana cewa kwanan nan ne muka sayar da man jiragen sama da ya kai cikin jiragen ruwa biyu ga kamfanin Saudi Aramco,” in ji shi.
Tun lokacin da ta fara aiki a shekarar 2024, matatar Dangote na ci gaba da ƙara yawan ɗanyen man da take tacewa a kullum inda yanzu take tace ɗanyen man da ya kai ganga 550,000 a rana.
Shugaban cibiyar NESG, Mista Niyi Yusuf, ya ce Nijeriya na buƙatar irin wannan zuba jarin domin cim ma burin haɓaka tattalin arziƙinta zuwa dala tiriliyan ɗaya.
“Domin cim ma tattalin arziƙin da ya kai dala tiriliyan ɗaya, dole yawancin jarin ya zo daga cikin gida. Na yi wargi a lokacin da muke cikin motar bas cewa yayin da wasu ke ƙirƙirar tsibirai domin nishaɗi, kun yashe cubic tonne miliyan 65 na ƙasa domin samar da makoma ga ƙasa. Wannan matatar, da wannan kamfanin takin zamanin da wannan harabar kamfanin gaba ɗaya da kuma ababen more rayuwa a nan ingantattu ne,” in ji shi.
Yusuf ya jaddada cewa irin waɗannan masana’antu na cikin gida suna da muhimmanci ga ci-gaban ƙarfin masana’antun Nijeriya kuma za su taimaka wajen haɓaka ƙananan masana’antu.
Ya ƙara da cewa cibiyar NESG za ta ci gaba da goyon bayan ingantaccen yanayi na zuba jari domin jawo hankalin masu zuba jari tare da haɓaka ci-gaba da tabbatar da samar da abinci da kuma magance matsalar rashin tsaro.
Ya nuna takaicin yadda Nijeriya ta kasance wurin jibge kayayyakin da aka ƙera daga ƙetare yana mai ƙarawa da cewa dole ƙasar ta tallafa wa ‘yan kasuwanta domin ta zama mai faɗa-a-ji a duniya.
Yusuf ya yaba wa manufar Dangote ta sa ƙasar ta fara cin gashin kanta a muhimman fannoni.