Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta fitar da wasu matakai na kauce wa fadawa hannun masu garkuwa da mutane a babban birnin tarayyar kasar.
Mai magana yawun rundunar Muyiwa Adejobi ne ya bayyana haka ranar Alhamis a yayin da yake gargadi ga al'ummar Abuja da sauran biranen Nijeriya game da karuwar matsalar masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
Muyiwa Adejobi ya bayyana haka ne a wani bidiyo da rundunar 'yan sandan ta wallafa a shafinta na X.
Sanarwar na zuwa a daidai lokacin da matsalar satar mutane a babban brinin kasar ke karuwa, lamarin da ke kara jefa fargaba a zukatan al'umma.
Sai dai hukumomin tsaro da gwamnati sun sha alwashin magance matsalar.
Domin kauce wa afkawa tarkon masu wannan mummunar ta'ada, Muyiwa ya bayyana wasu muhimman hanyoyi na rigakafi:
1. A tabbatar da cewa duk wata mota ko abin hawa da mutum zai shiga yana da rajista sannan gwamnati ta san da zamansa.
2. Ko wacce jiha da al'umma tana da tasha ko garejin mota da aka amince da shi, don haka a tabbatar da cewa an shiga mota a wuraren da aka ware domin jigilar tafiye-tafiye wadanda gwamnati ta san da zamansu, ''a daina shiga motar kyauta da ba za a biya kudi ba''.
3. Duk lokacin da aka bukaci motar haya ta Uber, a yi kokarin tantance lambar motar da wadda aka dora a kan manhajar don tabbatar da ita ce halatacciyar motar da aka aiko ta dauki mutum don gudun fadawa hannun 'yan "One Chance".
4. A rage fita daga gida cikin dare, sannan a kara sanya ido kan al'amuran da ke gudana a kewayenku don kare kai daga mugayen-iri a cikin al'umma.