'Yan takarar shugaban Nijeriya na manyan jam'iyyun ƙasar a zaben 2023 sun ce za su daukaka ƙara bayan kotu ta tabbatar da nasarar zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar LP sun yi taron manema labarai daban-daban ranar Alhamis suna masu bayyana matakin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a matsayin rashin adalci.
Atiku ya ce "na ki amincewa da hukuncin kotun ne saboda na yi amannar ba ta yi adalci ba", yayin da Obi ya bayyana cewa "muna mutunta hukuncin kotun, amma ba mu yarda da hanyoyin da ta bi wajen yanke shi ba."
Sai dai jam'iyyar APC mai mulki ta yi maraba da hukuncin wanda mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima, da ya halarci zaman shari'ar, ya bayyana a matsayin "nasara ga dimokuradiyya."
A ranar Laraba ne kotun ta yi watsi da ƙarar da 'yan takarar jam'iyyun hamayyar suka shigar a gabanta suna neman ta soke zaben da aka yi wa Bola Tinubu bisa dalilai daban-daban.
Alkalin da ya jagoranci yanke hukuncin, Mai shari'a Haruna Tsammani, ya ce matakin hukumar zaɓe na ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya ci zaɓen 25 ga watan Fabrairu, ya dace.
Sai dai Atiku Abubakar da Peter Obi sun ce za su daukaka kara zuwa Kotun Koli.
TRT Afirka ta tuntubi Barista Audu Bulama Bukarti, wani fitaccen lauya wanda ya yi mana karin bayani dangane da matakan da suka rage wa jam'iyyun hamayya a Nijeriya bayan hukuncin kotun da ya bai wa Shugaba Tinubu nasara a zaben 2023.
Zama da lauyoyinsu
Masanin shari'ar ya ce ya kamata 'yan hamayyar su fara zama da lauyoyinsu don su fahimci hukuncin kotun da dalilan da ta bayar na yin watsi da karar da suka shigar, domin sanin yadda za su dauki mataki na gaba.
'Suna da kwana 14'
Barista Bukarti ya ce 'yan hamayyar suna da damar daukaka kara idan ba su gamsu da hukuncin kotun ba, "amma wajibi ne su yi haka cikin kwana 14 bayan yanke hukuncin na ranar Laraba."
Labari mai alaka: Kotu ta tabbatar da Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya
Ya ce wannan tanadi yana cikin sashe na biyu na kundin da ke kula da daukaka karar zabe na Kotun Koli wanda aka zartar a shekarar 2023.
Bisa tanadin doka idan suka bari sai bayan kwana 14 suka gabatar da bukatar daukaka kara zuwa Kotun Koli, "ba za a saurari shari'ar ba, korar ta za a yi," in ji shi.
Daukaka kara zuwa Kotun Kolin
Fitaccen lauyan ya ce idan 'yan hamayyar suka daukaka kara zuwa Kotun Kolin Nijeriya a cikin kwana 14, to kotun za ta saurari korafinsu.
Ya ci gaba da cewa "ita kuma Kotun Kolin tana da kwana 60 ne ta yanke hukuncin karshe, kamar yadda sashe 285 karamin sashe na 7 na kudin tsarin mulkin Nijeriya ya bukata."
"Kwana 60 daga ranar da aka yanke hukuncin, ba daga ranar da aka shigar da daukaka kara Kotun Koli ba," kamar yadda masanin shari'ar ya yi karin haske.
Abin da zai biyo bayan hukuncin Kotun Koli
A karshe Barista Bukarti ya ce idan Kotun Koli ta yanke hukunci nan da kwana 60, "to daga nan kuma duk wanda hukuncin bai masa dadi ba, babu zancen daukaka kara, sai dai ya yi Allah Ya isa – shi ya sa ma wasu suke kiran Kotun Koli da sunan daga ke sai Allah Ya isa."