Sama da kashi 95 na 'yan kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ne suka amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda zai bayar da dama a tsawaita wa'adin mulkin shugaban kasa.
Kwamitin da ya gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a na kasar ne ya bayyana haka ranar Lahadi.
Kashi 95.21 na kusan mutum miliyan biyu da suka yi rajista ne suka amince da sabon kundin tsarin mulkin, in ji kwamitin da ya gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a.
Sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'ar da aka gudanar ranar 30 ga watan Yuli 30 na wucin-gadi ne, a cewar kwamitin.
Sabon kundin tsarin mulkin ya bayar da dama ga Shugaba Faustin-Archange Touadera, wanda aka sake zaba a 2020, ya tsaya takara karo na uku.
Masu hamayya da Touadera, wadanda suka yi zargin cewa yana so ya ci gaba da mulki tsawon rayuwarsa, sun soki kuri'ar jin ra'ayin jama'ar wadda ta soke dokar wa'adi biyu ga kowanne shugaban kasa tare da tsawaita wa'adin shugaban kasa zuwa shekara bakwai daga shekara biyar.
Kungiyoyin fararen-hula da masu dauke da makamai sun yi kira ga 'yan kasar su kaurace wa kuri'ar jin ra'ayin jama'ar.
Sai dai an gudanar da zaben "a yanayi na kwanciyar hankali," a cewar masu sanya ido na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Tsakiyar Afirka ta Economic Community of Central African States (ECCAS).
A baya Touadera ya ce Rasha da Rwanda za su "taimaka" wurin tabbatar da tsaro yayin kuri'ar jin ra'ayin jama'ar.