Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Nijeriya DSS ta ce tana bibiyar abubuwan da suke faruwa na tsara zanga-zangar da wasu mutane da kungiyoyi ke shirin yi a sassan kasar nan a makonni masu zuwa “wadda har yanzu masu hannu a shiryata ba su bayyana kansu ba.”
A sanarwar da ta wallafa a shafinta na X a yau Ahamis, DSS ta ce duk da cewa ta san cewa ‘yan ƙasa na da damar yin zanga-zanga, amma ta bankaɗo shirin da wasu ke yi na amfani da damar don “tayar da mummunan rikici a ƙasar”.
An shafe kwanaki batun zanga-zangar da ake son yi a Nijeriya tana yamutsa hazo, inda kawuna suka rarrabu a ƙasar, wasu na goyon baya yayin da wasu kuma suke cewa babu amfanin yin ta.
Masu son a yi din na cewa yanayin matsain tattalin arziki da ake ciki ne babban dalilin yin ta. Amma masu adawa da ita suna cewa yawanci zanga-zanga a Nijeriya ba abin da take jawowa sai rikici da tarzoma.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun daraktan watsa labaran hukumar, Peter Afunanya “masu shirya zanga-zangar na son yin amfani da tashin hankalin da lamarin ka iya jawowa don shafa wa gwamnatin tarayya da na jihohi kashin kaji da jawo musu baƙin jini da kuma haɗa su faɗa da talakawa.”
Kazalika ta ce ta gano cewa dalilin son yin zanga-zangar na da alaƙa da siyasa.
Ge jerin sauran abubuwan da DSS ta ce ta bankaɗo a shirin zanga-zangar:
- An gano masu bayar da kuɗaɗe
- Masu tallafawa
- Wadanda ake haɗin gwiwa da su a shirin.
Amma DSS ta ce ta fahimci cewa ba ƙarfi ya kamata ta yi aiki da shi ba a matakin farko wajen tafiyar da lamarin.
“A madadin haka sai muka bijiro da matakai da dabarun warware rikice-rikice daban-daban, gami da sauya tunanin masu kitsawa da haɗa gwiwa da masu ruwa da tsaki da sauran hanyoyin diflomasiyya, don hana masu tsara shirin aiwatar da manufar da ba a so,” in ji DSS.
Bayan haka DSS ta gargadi ƙungiyoyin da ke shirya zanga-zangar da cewa kada su yarda su jawo abin da zai jawo rashin doka da oda a ƙasar.
Sannan ta nemi masu shirya zanga-zangar da su saurari kiran da hukumomi suke musu su kuma yi haƙuri tun da har gwamnati ta yarda cewa ta fahimci halin tsananin da ake ciki kuma za ta yi wani abu.
“Hakan yana da muhimmanci saboda zanga-zanga ba abin da za ta jawo sai rikicin da zai jawo asarar rayuka da dukiyoyi da kawar da hankali gwamnati. Suna iya bin wasu hanyoyin don kai ƙorafinsu ba sai sun yi bore ba.”