An shafe sama da mako guda ana fama da rashin wuta a arewacin Nijeriya. / Hoto: Others

Yayin da aka shafe fiye da mako ɗaya ana fama da matsalar ɗaukewar wutar lantarki a arewacin Nijeriya, tuni wasu manyan ‘yan siyasar ƙasar suka soma ƙorafi dangane da halin da aka shiga.

Kamfanin da ke dakon wutar lantarki a ƙasar wato TCN ya ce an samu ɗaukewar wutar lantarki a yankin ne saboda lalata babban layin wutar lantarki da ya taso daga Shiroro zuwa Kaduna da wasu ’yan bindiga suka yi, wanda shi ne yake bai wa yankin arewacin kasar wutar lantarki.

Lamarin ya shafi harkokin kasuwanci da na asibitoci da ma sauran ɓangarorin gudanar da rayuwa.

A wata sanarwa da tsohon shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na X, ya ce matsalar wutar lantarki a Nijeriya babban abin damuwa ce.

“Duk ma’aikatar gwamnati da ke da alhakin shawo kan matsalar dole ne ta yi gaggawar shiga tsakani tare da mayar da wutar lantarki a yankunan da ke cikin mawuyacin hali,” in ji Atiku.

Haka kuma Atiku ya yi kira kan a bayar da ƙwarin gwiwa ga ‘yan kasuwa da su zuba jari ta ɓangaren samar da wutar lantarki.

Shi ma tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a Jam'iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna rashin jin daɗinsa dangane da wannan batu.

“Wani abin takaici ne yadda a yau wasu sassa na Arewacin Nijeriya suka shiga duhu sakamakon ɓarnar da aka yi a kan muhimmin layin wutar lantarki na Shiroro zuwa Kaduna mai karfin 330kV da ke samar wa jihohin Kano da Kaduna da kuma wani layin da ke samar da Bauchi da Gombe da sauran sassan arewa maso gabas.

“Wannan lamari dai ya kara ta’azzara ne sakamakon tsadar man fetur da dizal a Nijeriya, lamarin da ya kara jefa gidaje cikin duhu tare da tilasta rufe masana'antu,” in ji Kwankwason.

Tun bayan faruwar matsalar ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu da iyalai da sauran harkokin yau da kullum a arewacin kasar sun shiga halin-ni-’ya-su kasancewar yadda abubuwa da dama suka dogara kan wutar lantarki a wannan zamani.

A baya idan aka samu daukewar wutar lantarki na tsawon lokaci a kasar, wasu ’yan kasar musamman masu sana’o’i hannu kamar teloli da masu aski da sauransu sukan sayi man fetur ne don su ci gaba da sana’o’insu kafin a samu wutar lantarkin.

Sai dai a wannan lokaci hakan yana yi wa masu sana’o’i wahala kasancewar man fetur kansa shi ma farashinsa ya yi sama sosai, inda yanzu ake sayar da lita daya a kan akalla naira 1,000.

TRT Afrika