Manyan hafsoshin soji na kasashe kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, sun isa hedikwatar tsaron Nijeriya da ke Abuja don yin taro kan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.
Taron, wanda babban hafsan sojin Nijeriya Janar Christopher Musa yake jagoranta, yana samun halartar manyan hafsoshin sojin Togo, Senegal, Saliyo, Ghana, Liberia.
Sauran su ne manyan hafsoshin tsaron Guinea, Gambia, Cote Divoire, Jamhuriyar Benin da kuma Cape Verde.
Janar Christopher Musa ya shaida wa manema labarai gabanin taron cewa a shirye sojojin suke su motsa a duk lokacin da aka ba su umarni.
Labari mai alaka: Tarayyar Afirka ta bai wa sojojin Nijar wa'adin kwana 15 su mika mulki
Rahotanni sun ce babu wanda ya zauna a kan kujerun da aka ware wa hafsoshin sojin kasashen Gunea-Bissau da Mali da Burkina Faso da Nijar.
A makon jiya ne ECOWAS ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar wa’adin mako guda su mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki ko kuma su dauki matakai da suka hada da yin amfani da karfin soji.
Sai dai Janar Abdourahamane Tchiani, babban jami'in sojin da ya jagoranci juyin mulkin kuma ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban Nijar, ya gargadi kasashen waje game da yin katsalandan a harkokin cikin gida na kasar.
Kasashen Mali da Burkina Faso, da ke karkashin mulkin soji, sun lashi takobin yakar duk wata kasa da ta yi kokarin yin amfani da karfi a kan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.