Mafi yawan ‘yan cirani a Afirka na barin ar kasarsu ne don kokarin rabuwa da talauci/AA

Lokacin bazara ne a Moroko ranar 27 ga Oktoban 2013, lokacin da Sam Goncolo mai shekara 31 ya sauko daga jirgin saman da ya kai shi filin tashi da saukar jiragen sama na Kasa da Kasa na Mohammed V a birnin Kasabalanka.

Sam ya yi balaguro na nisan kilomita 2,000 daga Monrovia babban birnin Laberiya, don karatun nazarin Alakar Kasa da Kasa a Jami’ar Moroko.

Shirin Sam shi ne ya yi kaura zuwa Turai bayan gama karatunsa. Kamar mafi yawan ‘yan cirani, ya bar kasarsa don kokarin rabuwa da talauci tare da samun rayuwa mai inganci.

Amma ana yaudarar mafi yawan wadanda suke barin Laberiya da sauran kasashen Afirka kan hanyoyin da ake samun arziki da wuri.

A Laberiya, yaudarar da bayanan karyar da ake bayarwa sun samu ne saboda yanayin tattalin arzikin kasar da ke kokarin farfadowa daga illolin da ta fuskanta a lokacin yakin basasar da aka yi a tsakanin 1989 da 2003, da ya yi sanadin mutuwar mutum 200,000.

Hukumar Magance Gudun Hijira ta Kasa da Kasa (IOM) ta bayyana cewa, sama da ‘yan Laberiya 200,000 ne suke barin kasar a kowacce shekara don neman makoma mai inganci.

“Akwai jiran tsammani sosai a gida. Iyayena talakawa ne kuma ba sa aiki. Suna jiran na samu kudi da yawa a nan Turai,” in ji shi.

Amma bayan kamala karatunsa na jami’a, sai Sam ya sauya ra’ayi. Gaba daya ya yi watsi da burinsa na zuwa Turai ya koma gida Laberiya kawai. Sannan ya shawo kan sauran ‘yan cirani da dam aka su koma kasashensu.

Batun gaggawa a duniya

Bayan da Sam ya yi mu’amala da ‘yan cirani daga Afirka da suka makale a kasar ta Arewacin Afirka, sai ya fara dari-dari game da matakin ko ya ci gaba da zama a Moroko ko kuma ya tsallake tekun Bahar Rum zuwa Turai.

Ya zuwa 2023, Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai ‘yan cirani 22,000 a Moroko.

Babban Bankin Duniya ya ce kasashen Afirka shida – Aljeriya da Masar da Libiya da Moroko da Sudan da Tunisiya – sun zama muhimman cibiyoyin ‘yan gudun hijira da suke tafiya Turai.

Ya zuwa tsakiyar shekarar 2020, yankin Arewacin Afirka an kiyasta akwai ‘yan gudun hijirar kasa da kasa miliyan 3.2, kusan kashi 61 sun fito daga yankin ko wasu kasashen Afirka.

Sam ya shaida wa TRT Afirka cewa “Labaran da wadannan ‘yan ciranin suka ba ni da kuma irin wahalar da ake sha yayin tafiyar ne suka tsuma ni.

Na ga matasa masu basira da hazaka sosai, wadanda suke da abubuwa da za su kawowa kasashensu don cigaba, amma sai ga shi suna shan wahala a wannan tafiya mara dadi…. Duk a kan me?

Mummunar tafiya

A 2017, Hukumar Magance Gudun Hijira ta Kasa da Kasa ta rawaito mutuwar ‘yan cirani 44 sun mutu saboda kishin ruwa a lokacin da motarsu ta lalace a arewacin Nijar yayin yunkurin shiga Libiya don tafiya Turai.

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun bayyana cewa akwai mata da yara kanana daga cikin 44 da suka mutun.

Haka zalika a watan Disamban 2022, IOM din ta kara fitar da rahotin da ke bayyana a shekaru takwas da suka gabata yadda mutum sama da 5,600 suka mutu ko bata a yayin keta sahara, 103 daga ‘yan ciranin sun mutu a kasar Chadi.

A watan Afrilun 2022, Majalisar Dinkin Duniya ta ruwaito cewar sama da mutum 3,000 sun bata lokacin da suke yunkurin tsallaka tekunan Bahar Rum da Atlantika don isa Turai.

“Na ga halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki. Da yawansu ba su da matsuguni kuma suna kwana a sanyin sahara. Da yawa suna da yaran da ba su da lafiya. Na yi cudanya da su, da yawan su matasa ne masu kwazo.

“Da yawan suna da tsarin gudanar da kasuwanci mai kyau. Suna da dukkan abubuwan da za su sanya su samu nasara a kasashensu.“

“Amma an ba su bayanan karya inda suka fara wannan tafiyar da babu riba ko jin dadi a cikinta. Na yanke shawarar yin duk mai yiwuwa don dawo da su kan turbar gaskiya, hakan ya fara nasara har suka fara kama hanyar komawa gida.”

Haihuwar ‘ya mace da Sam ya yi ne ya kara karfafarsa kan komawa Laberiya.

“Na fahimci cewa bayan na kamala karatuna, idan har na ce zan tafi Turai, to zan zama kamar daya daga cikin wadannan, kama hanya mai hatsari inda zan kare a gantali ba tare da masauki ba, saboda ba ni da takardun shiga kasashen. Ba zan iya hakaito mummunan yanayin da zan jefa ‘yata ba idan na yi hakan.”

Alkaluma daga UNICEF kuma sun bayyana karuwar yawan yara kanana ‘yan gudun hijira daga kusan miliyan 24 a tsakanin shekarar 1990 da 2000 da kashi 50 wanda ya kama miliyan 36 a 2020.

UNICEF ta kuma yi hasashen a kowacce rana sama da yaro guda na mutuwa a hanyar tsakiyar tekun Bahar Rum daga Arewacin Afirka zuwa Italiya. A 2021 jumullar sama da ‘yan gudun hijira 29,000 ne suka mutu, in ji IOM.

Kingsley Okoye lauya ne kan gudun hijira a Nijeriya da ke Yammacin Afirka, ya fada wa TRT Afirka cewa “Da yawansu dole ce ke sa su tafiya saboda matsanancin yanayin tattalin arziki da al’amuran siyasa a kasashensu.”

A shekarar 2020 kadai ‘yan Nijeriya miliyan 1.7 ne suka bar kasar, kamar yadda Sashen Kula da Al’amuran Tattalin Arziki da Zamantakewa na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.

Kingsley ya kara da cewa “Wasu daga wadannan matasa sun sayar da dukkan abubuwan da suka mallaka don biyan kudin jirgi, suna masu fatan samun arziki a inda suka dosa.”

Bayanin Sam ya yi daidai da wannan batu

“Na zuba jari sosai a wannan tafiyar. Na sayar da komai. Shi ya sa yanke hukuncin komawa gida na da wahala. Na bar wannan mafarkin tare da komawa wajen iyayena talakawa, wadanda suke tsammanin na tara kudi da yawa. Na san za su samu karayar zuciya.”

A lokacin da karatun Sam ya kusa zuwa karshe, ya yi ta kokarin taimaka wa ‘yan gudun hijira da dama da suka shiga halin ni-‘ya-su.

“Na fada musu ina da buri a rayuwa kamar su don zuwa Turai, amma halaka kai ne yin kokarin tafiya ba tare da takardu ba.”

“Abu ne mai wahala jan ra’ayin wasu daga masu gudun hijirar kan su sauya shawara su koma gida. Da yawa sun ce ba za su iya hada idanuwa da iyalansu ba idan suka koma, gara su mutu a nan.”

Amma Sam ya ci gaba da zuwa wajen ‘yan gudun hijirar tare da wayar musu da kai. Ya yi aiki tare da kungiyoyin bayar da taimako da dama wajen bayar da gudunmowar tafinta. Akwai dokoki da dama da ake bi.

“Na rubuta wasikun neman daukar nauyi ga kungiyoyin bayar da tallafi na kasa da kasa don su gana da mu. Wadannan ganawa sun taimaka wajen tantance wasu daga ‘yan gudun hijirar tare da mayar da su gida.”

Wajen kula da takardun da suka jibanci doka, Sam ya ce karatunsa na alakar Kasa da Kasa ya taimaka matuka gaya.

Tunkarar gaskiya

Amma bayan ya kammala karatunsa, lokaci ne da Sam zai hadu da iyalansa. “Ana gobe zan tafi, ban iya bacci ba.

A watan Afrilun 2021 ne na dawo gida Laberiya tare da ‘yata, wadda a lokacin take da shekara uku.”

“Mutanen da suka san ni sun yi mamakin gani na. Iyayena da abokaina sun dinga tambaya ta me ya sa? Suna tsammanin abubuwa da dama. Da na zama mai kudi sosai. Na ga yadda suka damu sosai.”

Daga baya iyalan Sam suka amince da matakin da ya dauka, amma aka ci gaba da nuna masa wariya yayin gudanar da manyan taruka a dangi, musamman ma wasu na nesa da shi.

“Akwai abubuwan nuna wariya da dama. Ba na bukatar fadar su. Ina jin su a jikina. Abu ne da ke dugunzuma ni, musamman a lokacin da nake kokarin kula da ‘yata, wadda jim kadan bayan dawowar mu ta fara rashin lafiya saboda sauyin yanayi da muhalli. Na so tambayar dangina kudi, amma ban san wanda zan tambaya ba.”

Samun dama

Nan da rayuwa ta fara haskawa Sam. Bayan ‘yan watanni da komawar sa, sai IOM a Laberiya suka tuntube shi tare da ba shi aikin kula da mutanen da suka dawo Laberiya inda yake ba su shawarwari da kulawar kwakwalwa.

A yanzu yana aiki a matsayin mai bayar da shawarwari a karkashin shirin, yana kokarin hada ‘yan cirani da mahukuntan IOM a kasashen da suka je.

“Bayan na dawo na samu karfin gwiwa a zuciyata. Na yi farin cikin yadda labarina ya sauya.”

Shirin Warakar Kwakwalwa da Sasantawa ya kamkama a Laberiya, suna bayani a gidajen rediyo tare da bayar da takardun da ke kunshe da bayanai a ko yaushe don gargadar mutane kan su guji tafiya ba bisa ka’ida ba.

Rabaran Philip Nushan da ke shugabantar Shirin Gaskiya da Sasantawa ya fadawa TRT Afrika cewa “Da wahala a sauya tunanin ‘yan ciranin da suka dawo bayan zuciyarsu ta karye.”

Ya ce “Kin aminta da wariyar da ake nuna musu a cikin al’umma shi ne mafi muni. Ana musu kallon rashin nasara. Da yawa suna kokarin kashe kawunansu, dole ne a sanya musu idanu. Dole ne al’ummarmu ta zama mai yafiya.”

Rabaran Nushan da ma’aikatansa a wannan waje suna aiki da masana halayyar dan adam wajen horar da wadanda suka dawo da sana’o’in da za su taimaki rayuwarsu.

“Muna damuwa a lokacin da muka ji ahalinsu na fada musu munanan maganganu. Muna kokarin zama sabbin iyalansu, kuma wannan ya taimaki da yawan su don samun lafiya.”

Sam ya ce rayuwarsa ta dawo daidai. Kwanan nan ya gama karatuttuka guda biyu kan gudanar da otel da yawon bude ido da kula da baki.

“Saboda na aminta da kasata sosai da abun da za ta iya bai wa duniya. Na yi imanin wata rana duniya ce za ta dinga gogayya da Laberiya, ina nan ina jira….”

TRT Afrika