Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta Jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta tabbatar da Bala Mohammed Abdulkadir Kaura a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar.
Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, inda ta kori karar Air Marshal Siddique Abubakar na jam'iyyar APC ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala na Jam'iyyar PDP.
Tun ranar 18 ga watan Maris na 2023 aka gudanar da zaben jihar, sai dai APC ta shigar da kara tana kalubantar hakan.
Kotun, mai tawagar alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari'a wacce P.T Kwahar, ta ce ta kori karar ne saboda rashin ƙwaƙƙwaran dalilin da zai sa ta soke zaben, saboda an gudanar da shi bisa turbar da doka ta tanada.
A jawabin da ya gabatar jim kadan bayan yanke hukuncin, Gwamna Bala ya bayyana farin cikinsa kan abin da ya kira "adalcin da kotu ta yi."
"Muna godiya ga Allah SWT da ya ba mu dama ta jagorancin jihar Bauchi kuma yau kotu ta sake tabbatar da cewa komai da aka yi an yi cikin gaskiya da adalci.
"Wannan ba karamin lokaci ba ne na nuna farin ciki da godiya ga Allah da shugabanninmu musamman ma na jam'iyyar PDP da sauran wadanda suka ba da gudunmawa," in ji gwamnan.
Ya ci gaba da cewa "Lallai an yi gwagwarmaya, an shiga an fita, amma haka siyasa take. Bayan siyasa abin da ke gabanmu ita ce Bauchi, Bauchi, Bauchi da kuma Nijeriya.
"Shugabanci ba wasa ba ne, mun san wadanda suka taimaka mana, mun san wadanda ba su taimaka mana ba, amma dai kowa ma kansa yake so idan lokacin zabe ya zo.
"Su wadanda muka yi gwagwarmaya da su, muna ba su girma da kima, kuma muna musu nasiha su yarda da Allah shi ke ba da mulki, shi Ya ba mu wannan dama kuma ita ma jarabawa ce.
Su ajiye makamansu su zo mu yi aiki mu gina sabuwar Bauchi inda babu ƙyamar kowa, inda babu gaba da ƙiyayya, yadda zai kasance mun kawo hoɓɓasa kan ƙudurinmu na 'My Bauchi Project' tun farko da ya sa mutanen Bauchi suke kaunarmu."