NLC ta buƙaci gwamnatin Nijeriya ta gaggauta janye jami’an tsaro daga hedikwatar ta, inda ta ce dole a kawo ƙarshen wannan cin zali.''/ Hoto: Reuters

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa a Nijeriya (NLC) ta bayyana cewa jami’an tsaro ɗauke da muggan makamai sun yi dirar-mikiya a hedikwatarta da ke Abuja wato Labour House.

''A ranar Laraba da misalin karfe 8:30 na dare gomman jami’an tsaro ɗauke da makamai sun kai wa ginin Labour House hari,'' a cewar wata sanarwa da NLC ta fitar a safiyar Alhamis.

''Gomman jami'an tsaro sanye da kayan soja da na gida sun kai hari Labour House inda suka kutsa kai a hawa na biyu da na goma kana suka yi awon-gaba da wasu takardu a cikin motocinsu, suna ikirarin cewa wai ana amfani da takardun wajen rura wutar zanga-zangar da ake yi Nijeriya.''

''Jami'an sun kwashe ɗaruruwan litattafai da sauran maƙaloli," in ji sanarwar da ke ɗauke da sa hannun shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na NLC, Benson Upah ya fitar.

"Jami'an tsaron sun yi ikirarin cewa suna neman wasu takardu da kayayyaki da aka yi amfani da su wajen rura wutar zanga-zangar #EndBadGoveranance da ake yi a Nijeriya."

Kawo yanzu dai ƙungiyar NLC ba ta kai ga tantance yawan abubuwan da jami'an suka kwashe daga ofishinta ba.

Kazalika NLC ta buƙaci gwamnatin Nijeriya ta gaggauta janye jami’an tsaro daga hedikwatar ta, inda ta ce dole a kawo ƙarshen wannan cin zali.''

Lamarin dai ya faru adaidai lokacin da 'yan Nijeriya suke ci gaba da gudanar da zanga-zangar kwana 10 kan neman a kawo ƙarshen tsadar rayuwa a ƙasar, inda a yau aka shiga kwana ta kakwas.

TRT Afrika