Hukumomi a N’Djamena babban birnin kasar Chadi sun tabbatar da cewa jakadan Jamus, wanda aka ba shi wa’adin sa’o’i 48 ya fice daga kasar, ya bar Chadi.
A ranar Juma’a ne gwamnatin soji ta Mahamat Idriss Deby Itno ta bukaci jakadan ya yi gaggawar ficewa daga kasar bayan ta zarge shi da saba ka’idoji da kuma ‘rashin da’a ga harkokin diflomasiyya’.
“Jakadan Jamus a Chadi Jan Christian Gordon Kricke ya yi amfani da jirgin Air France a ranar Asabar da dare,” kamar yadda ministan harkokin wajen Chadi Mahamat Saleh Annadif ya sanar.
Haka kuma kakakin gwamnatin kasar Aziz Mahamat Saleh ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP da ficewar jakadan.
Hukumomi a kasar ba su bayyana asalin dalilin da ya sa aka kore shi ba.
Sai dai wani jami’in gwamnatin Chadi, wanda ba ya so a bayyana sunansa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa jakadan ya cika “katsalandan” kan harkokin gudanar da gwamnati a kasar da kuma wasu maganganu da ya yi da za su iya “raba kan ‘yan kasar Chadi”.
Wani jami’in ma’aikatar harkokin waje ta Jamus a ranar Juma’a ya bukaci dalilai na korar jakadansu wanda yake rike da mukaminsa tun watan Yulin 2021.
Tsawaita mulkin Itno
Shugaba Mahamat Itno, ya karbi mulki a ranar 20 ga watan Afrilun 2021 bayan mutuwar mahaifinsa Idris Debby wanda ya jagoranci kasar tsawon shekara 30.
Gwamnatin riko wadda Mahamat ke jagoranta ta yi alkawarin mika mulki ga gwamnatin farar-hula ta anyar gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci sai dai a watan Oktoban bara an kara wa’adin Mahamat da shekara biyu.
Jakadan kasar Jamus na daga cikin wadanda suka taya takwarorinsa na Faransa da Sifaniya da Netherlands nuna rashin jin dadi kan jan kafa wurin mayar da mulki ga farar hula.