Daga Abdulwasiu Hassan
“Idan ba ka san gaskiyar yadda Amurka take ba, za ka je ne da kuskuren tunani.”
Wannan shi ne sakon wani bakin Ba’amurke wanda ya dauki matakin da ba a saba gani ba, na barin aikinsa a hukumar sojin Amurka, kuma ya koma kasar Gambiya da ke Yammacin Afirka don zama manomi.
Rick Devon Usumbura, wanda ya yi hijira ya koma Afirka shi da iyalansa a shekarar 2016, ya fada wa TRT Afirka cewa ya yi imanin Afirka ta fi dacewa da rayuwa mai dadi fiye da Turai ko Amurka.
Wannan wani gagarumin abu ne da ya sabawa yadda aka saba ganin masu hijira daga Afirka zuwa Turai ko Amurka, yawanci matasa ‘yan ci-rani.
Da yawa daga bakin haure sukan bi hanyoyi masu hadari, ta cikin Hamadar Sahara, da kuma Bahar Rum, a yunkurinsu na neman damarmakin kyakkyawar rayuwa a Turai.
A ta bakin kungiyar jin-kan yara ta Save the Children, kusan mutum rabin miliyan ne, ko dai suka tsallaka ko suka yi kokarin tsallakawa Turai ta Bahar Rum, tun shekarar 2019.
A wani rahoto da aka fitar a watan Fabrairun da ya gabata, kungiyar jin-kan ta ce bakin-haure 8,468 ne ko dai suka mutu, ko suka bata yayin kokarin tsallaka teku, yawancin a kan kananan jiragen ruwa. Sannan kuma dubbai sun yi nasarar ketarawa ta sahihiyar hanya.
Rick Doven wanda dan shekara 59 ne, ya yi imanin cewa damarmakin kyakkyawar rayuwa sun fi samuwa a Afirka, sama da abin da masu barin Afirka suke hari. Jim kadan bayan isarsa Gambiya, ya sayi filin noma ya kafa gonarsa mai suna, “The Black Acres of the Gambia”.
Da farko, matarsa mai suna Cynthia tare da yaransu hudu sun soki tunanin zama a kasar, amma ya ci nasarar gamsar da su. Yanzu dukansu suna zaune a cikin farin ciki a wannan kasa wadda ake saka ta a jerin kasashen da ake yawan zuwa yawon bude-ido.
Yayin da yake gutsurar dan icen da ya tsunko daga bishiyar da ke gonar tasa, Rick Doven ya ce, “Kuna ji, na sha yin mafarkin samun irin wannan rayuwa, wato na yi tattaki kan kasar da na mallaka, ba sai na tsallaka katangar wani ba.”
A wani bidiyo da matarsa ta dauka kuma ta dora a tashar YouTube, an nuno Rick cikin annashuwa yana cewa yanzu ina iya “cin abinci kurum, da duk irin kayan marmarin da nake son ci”.
"Mafarkin nasara a Amurka” ya koma wasikar jaki"
An haifi Rick a garin Dublin da ke jihar Georgia ta Amurka.
Iyayensa sun tafi da shi garin Chicago inda suka zauna a can, a wani zamani da aka kira da zamanin Gagarumar Hijira, yayin da kusan bakaken fata miliyan shida suka yi kaura daga kauyukan kudancin Amurka, zuwa biranen arewacin kasar, a shekarun karni na 20.
Daga bisani, bayan ya girma, Rick ya shiga rundunar sojin Amurka. Amma bayan shekaru 15 a aikin soji, ya ajiye aiki a matsayin Saja na mai kula da karamar runduna.
Rick Doven ya fada wa TRT Afirka cewa ya fice daga aikin soji saboda “raunin lafiyarsa” da kuma gajiyawarsa na ci gaba da hakuri da fuskantar banbancin launin fata a wajen aiki.
Ya kafa kamfanin tsaftace gidaje a Amurka, kafin ya yi kaura zuwa Gambiya da ke Afirka, tare da iyalansa.
Rick ya ambata cewa ya samu kwarin gwiwa daga maganganun tsohon shugaban Gambiya, Yahaya Jammeh, game da kishin Afirka.
A maganganun Shugaba Jammeh, ya nemi ‘yan Afirka su kara kokarin zamowa masu dogaro da kai wajen samar da abinci.
“Dalilin da ya sa muka yanke shawarar dawowa Afirka shi ne babu wani Mafarkin Amurka. Kawai dai akwai Kukumin Amurka”.
Zarge-zargen nuna bambancin launin fata a hukumomin tsaron Amurka ya ci gaba da maimaituwa a shekarun baya-bayan nan.
Hakan na faruwa a cikin mu’amalar yau da kullum da kuma yadda ake mu’amalantar bakake a rundonar soji, da ma fararen hula.
Mafi shahara shi ne kisan bakin mutumin nan George Floyd, a shekarar 2020, wanda ya haifar da zanga-zanga a tituna da kuma Allah wadai daga gun al'ummun duniya.
Biyo bayan kisan Floyd, shugaban hafsosin sojin Amurka, General Mark Milley, ya bayyanawa kwamitin Majalisar Wakilan Amurka mai lura da Hukomomin Soji, cewa, ba a amince da “bayyanar duk wata alama ta nuna bambancin launin fata ba, ko nuna son kai, ko fifita wani” a cikin rundunonin tsaron Amurka.
Matarsa Rick, Cynthia ta sanar da TRT Afirka cewa da yawa daga ‘yan Afirka da ke yunkurin yin hijira, ba su da masaniyar gaskiyar lamari a Amurka.
“Kawai za ka so a ce ka je can, kana tunanin tarar da abin da kake gani a talabijin, wanda yaudara ce da ke kawar da tunanin mutane game da Amurka”.
Maigidan nata, shi ma ya karfafa wannan, inda ya ce yayin da masu hijira suka isa Amurka, sau da yawa sukan ga ba “yadda ake zuzuta take ba”.
Ma’auratan biyu sun ce labarinsu yana ba da ma’ana wajen bakaken Amurka da yawa, wadanda suke fuskantar bambancin launin fata.
A fadinsa, Rick ya ce hijirarsu ta tsuma adadi da yawa na ‘yan asalin Afirka don su koma zuwa nahiyar, su baro Amurka da Turai.
Rick ya kara da cewa, "akwai ‘yan Gambiya da dama da suka koma gida sakamakon mun nuna musu bambanci tsakanin rayuwa a Gambia, da kuma a Amurka.
"Yawancinsu sun baro Amurka da Jamus da Burtaniya, da wasu wuraren saboda damarmakin da suka gani a nan”.
Tunkarar kalubale a Afirka
A can gonar tasa, Rick ya ce a yanzu ya fi ganin gonarsa a matsayin wani “lambu”, a maimakon wata gonar aiki. Yana fatan inganta ta nan gaba, don fara noman abinci a gargajiyance, da kuma dabbobi don kasuwanci.”
Sai dai Cynthia da Rick sun yarda cewa suna fuskantar kalubale a Gambiya. Kasancewar sun girma a Amurka, inda ake da ababen more rayuwa, babbar matsalarsu a Gambiya ita ce rashin lantarki mai tabbas. Sannan rashawa ma wata babbar matsala ce.
Rick ya ce, “Da za mu iya rage rashawa a nahiyar Afirka, kuma a fara biyan albashi mai kyau, da an dauki hanya”.
Haka nan, ya yi amanna cewa wannan zai taimaka matuka wajen rage guguwar hijira daga Afirka.
Duk da dai Amurka tana da cigaba sosai, sama da duk wata kasar Afirka, Rick yana da kyakkyawan fata game da samun sauyi mai kyau a nahiyar. Ya yi amanna cewa kalubalen da ake fama da su “ba su kai munin jure mummunar rayuwa a Amurka ba”.
Ya ce, “Babu inda babu matsala. Gara nan ina iya sauke kafata a inda ake samun kyautatuwar al’amura, maimakon dankarewa a wajen da lamura ce tabarbarewa. A gaskiyar zance, Afirka ita ce makomar duniya”.