Kasar Italiya ta taimaka wa Jamhuriyar Nijar da kudi sama da biliyan biyu na CFA domin bunkasa noman tumatur a kasar.
Italiya ta yi hakan ne da nufin shawo kan matsalar tsadar tumatur ko kuma yankewar sa a kasuwanni da ake gani a wasu lokutan a cikin shekara a Nijar din.
Wannan shirin bunkasa noman na tumatur a karkashin wannan tallafi na Italiya, ya kuma tanadi kaddamar da aikin noman tumatur a lambuna da fadinsa ya kai eka 100.
Za a samar wa manoman wata hanyar ban ruwa ta hanyar amfani da hasken rana, musamman a jihohin Tawa da Maradi.
Jamhuriyar Nijar na samar da tumaturin ne ta hanyar noman rani kawai, hakan ya sa ake yawan fuskatar karancinsa a lokuta da dama ciki kuwa har da lokacin damina.
Nijar tana da Kogin Isa da ya ratsa kasar har na tsawon kilomita 550 wanda yake taimaka wa wajen noman rani.