Monday Okpebholo  ya yi nasarar cinye ƙananan hukumomin 11 daga cikin 18, yayin da Asuerinme Ighodalo ya samu ƙananan hukumomi bakwai, amma Olumide Akpata na LP bai ci ko da rumfar zaɓensa ba./Hoto: OTHER

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Nijeriya (INEC) ta ayyana Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin mutumin da ya lashe zaɓen gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ƙarshen mako.

Yayin da yake sanar da sakamakon zaɓen, babban jami'in hukumar zaɓen Edo, Farfesa Faruk Adamu Kuta ya ce Monday Okpebholo na APC ya samu ƙuri’a 291,667, yayin da Asuerinme Ighodalo na jam’iyyar PDP mai mulkin jihar, ya samu ƙuri’a 247, 274 a zaɓen.

"Monday Okpebholo na APC ya lashe zaɓen gwamnan jihar Edo da aka gudanar ranar 21 ga watan Satumban 2024 bayan ya samu ƙuri’u mafi rinjaye tare da cika duka sharuɗɗan da hukumar zaɓe ta gindaya," a cewar Farfesa Kuta.

Monday Okpebholo ya yi nasarar cinye ƙananan hukumomin 11 daga cikin 18, yayin da Asuerinme Ighodalo ya samu ƙananan hukumomi bakwai, amma Olumide Akpata na LP bai ci ko da rumfar zaɓensa ba.

TRT Afrika