Hannatu Musawa ta ce babu ta inda ta saba dokar Nijeriya. Hoto/ Hannatu Musawa

Ministar Al’adu da Fasaha ta Nijeriya Hannatu Musa Musawa ta mayar da martani kan ce-ce-ku-cen da ake yi cewa nadin da aka yi mata a matsayin minista alhali tana yi wa kasa hidima ya saba dokar kasar.

A wata sanarwa da ministar ta fitar, ta tabbatar da cewa tana yi wa kasa hidima kuma ta kalubalanci masu ce-ce-ku-ce kan cewa babu ta yadda ta saba dokar Nijeriya.

“Ina so na bayyana karara cewa sabanin maganganu da kuma zato na karya da ake yadawa a kafafen sada zumunta inda ake zarge-zarge na karya, babu wani wuri da aka saba doka ko kundin tsarin mulkin Nijeriya kan matsayina na minista da kuma mai yi wa kasa hidima,” kamar yadda ta bayyana.

“Dole ne a bayyana cewa babu wata doka a Nijeriya ko ta NYSC da ta hana shugaban Nijeriya nada mutumin da ke yin hidimar kasa kan mukamin siyasa.

“Haka kuma babu wani sashe na dokokinmu da na NYSC da ya ce dole mai yi wa kasa hidima ya kammala hidimar kasarsa kafin a ba shi wani mukamin siyasa.

Babu wata doka ko kuma wata iyaka daga kundin tsarin mulki kan haka. Ban saba wata dokar Nijeriya ba,” in ji Hannatu Musawa.

“Hasali ma a wani hukunci da Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya ta yanke a 2021, Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya yanke hukunci kan cewa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ba ya bukatar mutum ya bayar da takardar digirin farko ko wata takardar shaidar karatu har da ta NYSC kafin ya zaman minista a Nijeriya.”

Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun irin wannan takaddama kan batun yi wa kasa hidima ba game da masu rikie da mukamai na siyasa.

Domin ko a 2018 sai da Ministar Kudi ta Nijeriya Kemi Adeosun ta ajiye aiki sakamakon takardar NYSC ta bogi.

Haka kuma sai da aka yi ta takaddama kan tsohon ministan sadarwa na Nijeriya Adebayo Shittu kan cewa bai yi NYSC ba.

TRT Afrika