Asusun Bayar da Lamuni na Duniya wato IMF ya taya Nijar murna tare da jinjina ga ƙasar sakamakon hasashen ci gaban tattalin arziki da Nijar ɗin za ta samu a nan gaba.
IMF ya ce yana sa rai ƙasar za ta samu bunƙasar tattalin arziki da kaso 8.8 zuwa ƙarshen shekarar 2024 tare da hasashen cewa ƙasar za ta ci gaba da ɗorewa kan ci gaban da take samu inda tattalin arziƙinta zai haɓaka a shekarar 2025 da kaso 7.9 cikin 100.
Daraktan IMF a Nijar Ouattara Wautabouna ne ya tabbatar da hakan a yayin wata tattaunawa da ya yi da Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine.
Ya yi maraba da irin matakan da Nijar ke ɗauka wurin haɓaka tattalin arziƙi da ci gaban ƙasar.
A baya-bayan nan ƙasar ta Nijar na ta ɗaukar matakai da nufin haɓaka tattalin arziƙinta, waɗanda suka haɗa da bunƙasa ɓangaren wutar lantarkinta inda ko a watan nan sai da ƙasar ta samar da sabuwar tashar wutar lantarki a Yamai, a bara kuma ta ƙaddamar da tashar sola mafi girma a ƙasar.
Haka kuma a makon nan ƙasar ta ƙaddamar da wata masana’antar sarrafa rodi da aka gina ta hanyar zuba jarin CFA biliyan biyu wadda za ta rinƙa samar da tan dubu 20 na rodi a duk shekara, tare da samar da guraben ayyukan yi ga matasan Nijar.
Irin waɗannan matakan da Nijar ɗin ke ɗauka na bunƙasa ƙasar ne ya sa IMF ɗin ta ce za ta ci gaba da bai wa Nijar goyon bayan da ya dace wurin aiwatar da ayyukan ci gaba a ƙasar.
Duk da raba gari da Nijar ta yi da ƙasashen yamma da wasu ƙungiyoyi na ƙasashen Yamman, tana ci gaba da ƙulla alaƙa mai ƙarfi da hukumar ta IMF domin ko a bana sai da ya sanar da sakin kuɗi na rance har dala miliyan 71 ga Jamhuriyar Nijar.