IMF - daya daga cikin cibiyoyi kalilan da ke ci gaba da bayar da agaji ga Nijar - ta yi nuni da cewa, ana sa ran tattalin arzikin Nijar zai ƙaru da kashi 10.6 cikin 100 a bana.

Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF ya sanar da sakin kudi na rance har dala miliyan 71 ga Jamhuriyar Nijar, wadda sojoji suka yi juyin mulki a bara.

Amincewar ta zo ne a daidai lokacin da kwamitin zartarwa na IMF ya kammala nazari na hudu da na biyar na tsarin ci gaba da ba da lamuni ga Nijar, da kuma nazarce-nazarce na farko na tsarin da aka yi a karkashin shirin ba da rance mai ɗorewa, wato Resilience and Sustainability Facility.

"Matakin ya ba da damar fitar da kusan dalar Amurka miliyan 71 a dunƙule," in ji IMF a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, lamarin da ya sa jumullar kudaden da aka kashe a karkashin yarjejeniyar biyu suka kai kusan dala miliyan 255.

Asusun ya ƙara da cewa, yayin da ake aiwatar da shirin "a karshen watan Yunin 2023," sai rikicin siyasa ya kawo cikas ga wannan lamarin, wanda ya haifar da tarin basussuka na waje da na cikin gida.

“Takunkuman da aka sanya wa Nijar bayan juyin mulkin waytan Yulin 2023 sun yi matuƙar yin tasiri kan tattalin arzikin Nijar,” in ji mataimakiyar manajan daraktan IMF, Antoinette Sayeh.

Ta ƙara da cewa, duk da haka, "hanyoyin tattalin arziki na kusa da na matsakaicin lokaci sun inganta sakamakon fara fitar da mai, da ɗage takunkumai, da kuma ƙaruwar noma."

Ta bukaci hukumomi da su dauki mataki kamar sake gina hanyoyin samar da kudade da inganta tsarin kula da basussuka da bunƙasa tsare-tsaren yaƙi da cin hanci da rashawa.

IMF - daya daga cikin cibiyoyi kalilan da ke ci gaba da bayar da agaji ga Nijar - ta yi nuni da cewa, ana sa ran tattalin arzikin Nijar zai ƙaru da kashi 10.6 cikin 100 a bana.

AFP