'Yan bindiga sun hallaka jami'an gwamnati uku da sojan da ke musu rakiya a kudu maso yammacin Nijar, yayin da suke tsallakawa daga iyakar Nijeriya. Hukomomin Nijar sun tabbatar ranar Lahadi cewa abin ya faru ne a makon da ya gabata.
Rundunar sojin ta ce, "Ranar Laraba ne wani gungun masu ɗauke da makamai daga Nijeriya suka far ma motar, inda suka hallaka mutum huɗu", amma ba su fayyace waɗanda abin ya rutsa da su ba.
Sanarwar ta ce daga baya maharan sun "koma cikin Nijeriya". Mazauna yankin sun ce waɗanda aka kashe ɗin sun je ziyara ne Diffa, wani yanki da ya sha fama da yawaitar muggan hare-haren Boko Haram da ISWAP, tun 2015.
Yankin na Diffa yana kan gaɓar Tafkin Chadi, wanda ke tsakiyar ƙasashen Kamaru, Chadi, Nijar da Nijeriya. Tsibiran da ke tafkin sun zamo maɓoyar ƙungiyoyin jihadi masu ɗauke da makamai.
Kogin Komadougou Yobe, wanda ya raba Nijar da Nijeriya a baya ya taimaka wajen ba wa Diffa kariya daga hare-haren kan iyaka. Amma ruwan kogin ya yi ƙasa wanda ya haifar da "hanyoyin tsallakowa daga Nijeriya zuwa Nijar".
Sojin sun ce mayaƙan ISWAP na amfani da waɗannan hanyoyin wajen kai hari kan matafiya a titi, inda wannan harin kwanton-ɓauna ya faru a makon jiya.
Tun bayan faruwar lamarin, hukomomin yankin sun haramta motoci "musamman masu 4x4" daga tafiya ba tare da rakiyar soji ba a titin da ya fi samun hari, wanda ya kai tsayin kilomita 70, wanda ya haɗe garin Diffa da garin Maine Sorao.
Wani tsohon jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa 'yan kwanton-ɓaunar "sun fi harar manyan motoci masu tsada da ke iya bin kowane yanayi, wanda suke ƙwacewa don su sayar a Nijeriya".
A yankinTillaberi da ke yammacin Nijar, kusa da iyakar Burkina Faso da Mali, sojin Nijar suna yaƙi da wasu ƙungiyoyin jihadi masu alaƙa da Al-Qaeda da Islamic State.
Ranar Asabar, ɗaruruwan mutane sun yi zanga-zanga a Tillaberi, inda suke neman gwamnatin sojin Nijar ta kafa "rundunonin kai tallafin gaggawa" da "sansanin sojin sama", da ɗaukar farar-hula "'yan sa-kai" don taimakawa kare mutane daga hare-hare.
Gwamnatin sojin da ta ƙwace mulki a juyin mulkin watan Yuli na 2023, ta koka kan cewa gwamnatin farar-hula ta shugaba Mohamed Bazoum ba ta yi ƙoƙari ba wajen daƙile hare-haren 'yan ta'adda.