Hukumar OCRTIS na yawan kama masu safar miyagun kwayoyi a Nijar. / Hoto: OCRTIS 

Hukumar da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Nijar OCRTIS ta ce a 2022 jami’anta sun kama miyagun kwayoyi da kudadensu suka kai biliyan 26.

A sanarwar da kakakin hukumar 'yan sanda ta Nijar, Kwamishina Habou Mountari ya fitar, hukumar ta OCRTIS ta kama mutum 5,532 da take zargi da safarar miyagun kwayoyi.

A cewar sanarwar, mutum 210 a cikinsu mata ne sai kuma 454 ‘yan kasashen waje.

Sanarwar ta ce kasar ta Nijar ta kasance tamkar wata hanya da masu safarar miyagun kwayoyin ke amfani da ita wurin jigila zuwa kasashen Libiya da Aljeriya har zuwa kasashen Turai.

Hukumar ta kara da cewa kaso 5.62 na wadanda aka kama shekarunsu ba su haura 18 ba sai kashi 58.92 sun kama daga 18 ne zuwa 29.

Hukumar ta ce tana yin iya bakin kokarinta domin dakile safarar miyagun kwayoyin, sai dai masu safarar suna fito da sabbin dabaru a kullum na kauce wa shingayen bincikensu.

TRT Afrika