Hukumar kula da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta ankarar da duniya kan cewa kungiyoyin da ke dauke da makamai sun yi awon gaba da wasu abubuwa masu muhimmanci da kayayyakin tarihi a gidajen tarihi a Sudan mai fama da yakin basasa.
Hukumar UNESCO ta ce ta damu matuka game da rahotannin baya-bayan nan na yiyuwar sacewa da kuma lalata wasu gidajen tarihi da kayayyakin tarihi na kasar Sudan, ciki har da gidan adana kayan tarihi na kasa, da kungiyoyi masu dauke da makamai suka yi.
UNESCO ta ce tana sa ido kan tasirin yaƙi a a al'adun gargajiya na Sudan da cibiyoyin al'adu da masu fasaha tun bayan barkewar rikici a shekarar 2023.
"A cikin 'yan makonnin da suka gabata, wannan barazana ga al'adu ta kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba, tare da rahotannin sace kayan tarihi, wuraren tarihi da kuma tarin kayayyaki masu zaman kansu."
Tsofaffin kayayyaki
Ta ce ta damu matuka da rahotannin sace-sacen da aka yi a gidan adana kayan tarihi na kasar Sudan, da kuma gidan tarihin Khalifa House da ke Omdurman da kuma gidan tarihin Nyala a kudancin Darfur.
Gidan kayan tarihi na ƙasa, wanda aka buɗe a cikin shekarun 1970, yana ɗauke da abubuwa sama da 2,700 waɗanda suka haɗa da wasu mahimmai daga tsohuwar daular Fir'auna ta Masar da al'adun Nubian.
Hukumar ta UNESCO ta nanata kira ga jama'a da kasuwannin fasaha da ke da hannu a cikin cinikin kadarorin al'adu a yankin nan da ma duniya baki daya da su guji saye ko shiga cikin shigo da kaya ko fitar da su ko kuma mallakar kadarorin al'adu daga Sudan.
Hukumar ta ce tana shirin horas da jami’an tsaro da na shari’a na kasashen da ke makwabtaka da Sudan a birnin Alkahira nan da karshen shekara.
Wurare masu aminci
Tun a watan Afrilun 2023 ne yaki ya barke tsakanin sojojin kasar, karkashin jagorancin shugaban kasar Abdel Fattah al-Burhan, da kuma Rapid Support Forces (RSF), wanda tsohon mataimakin Burhan Mohamed Hamdan Daglo ke jagoranta.
Tun da aka fara fada, UNESCO ta ce tana goyon bayan daukar matakan gaggawa a wasu gidajen tarihi na tarihi guda biyar na Sudan, wadanda suka hada da tattara “kayayyakin da ke cikin hadari” da kuma samar musu amintaccen waje.