Hukumar da ke kula da gidajen rediyo da talabijin ta Nijeriya NBC ta maka wa gidan talabijin na Channels a kasar tarar naira miliyan biyar kan saba ka’idojin watsa labarai.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa NBC ta aika wa gidan talabijin din takardar tarar ne a sakamakon wani shiri na siyasa da aka yi da mataimakin dan takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar Labour Dr Datti Baba-Ahmed.
Takardar mai taken “Hirar tunzurarwa, saka takunkumi”, na dauke da sa hannun shugaban hukumar wato Balarabe Shehu Ilelah.
“Hukumar NBC ta kalli wata tattaunawa da aka yi kai tsaye da mataimakin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Labour, Dakta Datti Baba-Ahmed, wadda jagoran shirin Politics Today, Seun Okinbaloye ya jagoranta a ranar Laraba, 22 ga watan Maris.
“Dakta Baba-Ahmed ya bayana cewa za a saba wa kundin tsarin mulki idan aka rantsar da zababben shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, saboda kurakuran zabe,” in ji Ilelah a takardar.
Ya bayyana cewa wannan tattaunawar da aka yi za ta iya tunzura jama’a da tayar da zaune tsaye inda ya ce an saba wa wasu ka’idojin watsa labarai.
Ya ce hakan kuma ya hada sashen da ke cewa kada a watsa wani labari da zai iya tunzurawa ko kuma zai sosa zukatan jama’a ko kuma labaran na magana ne kan wani ko wata kungiya mai rai ko matacce ko kuma taba darajar bil adama.
Ya bayyana cewa sakamakon saba wadannan dokoki, gidan talabijin din zai biya N5,000,000 a karon farko.
Haka kuma ya ce duk wani abu irin wannan da ya sake biyowa baya zai jawo tarar da ta fi wannan.
Darakta Janar din na NBC ya ba gidan talabijin din mako biyu ya biya wannan tarar ko kuma hukuncin ya zarta hakan.