Hawan dawaki ya fi shahara a Kano inda ake gudanar da hawan dawaki  cikin shigar gargajiya da al'ada a lokacin bukukuwan sallah sau biyu a shekara. / Hoto: AA

Hukumar Raya Ilimi da Kimiyya da Al'adu ta Majlisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta sanya hawan dawaki da ake yi da sallah a Nijeriya cikin jerin bukuwan al'ada na hukumar.

A bikin na hawan dawaki wanda aka fara tun ƙarni na 15 a Kano, sarki, wanda shi ne jagoran addini yana yin hawa tare da mahaya dawaki fiye da 10,000 da suka haɗa makaɗa da mawaƙa, inda suke kewaya wasu sassan cikin birnin Kano, birni mafi girma a arewacin Nijeriya, wanda mafi yawan mazaunansa Musulmi ne.

Ana gudanar da baikin ne sau biyu a shekera; lokacin Ƙaramar Sallah da kuma lokacin Babbar Sallah.

Ana kuma gudanar da bikin - da aka fi sani hawa daba - a garuruwan Musulmai da dama a ƙasar Hausa.

'Fitatccen bikin mai ƙayatarwa'

Hawan na sallah ya samo asali ne daga Kano, birni na biyu mafi yawan jama'a a Nijeriya, inda sama da mutum miliyan huɗu ke rayuwa a cikinsa, wanda kuma shi ne birni mafi yawan Musulamai a Nijeriya, sannan sarkin Kano na daya daga jagororin Musulmai mafiya tasiri a ƙasar.

"Durbar biki ne mai ƙayatarwa, da mutunci, da alfahari da kuma nishaɗantarwa," a cewar Hajo Sani, wacce ke wakiltar Nijeriya a hukumar ta UNESCO, a yayin taron Kwamitin Haɗaka don Alkinta Bukukuwan Al'ada karo na 19 da aka gudanar a Asuncion, babban birnin Paraguay.

"Biki ne na al'ada mai ƙarfin gaske wanda yake haɗo ƙabilu da dama, da suka haɗa da Hausawa, da Fulani, da Larabawa, da Nufawa, da Yarabawa da Abzinawa, abin da yake haɗa su su zama al'umma ɗaya,"kamar yadda ta bayyana.

A yayin bikin, sarki, wanda ke yin shiga ta ƙasaita shi ne yake jagorantar hawan, inda dogarai da hakimai da dakaru suke yi masa rakiya a duk lokacin hawan.

Abin da ya sa aka hana hawa a babbar sallar da ta gabata

Sarkin da sauran mahaya suna kewaya wasu sassan Kano, yayin da jama'a suke yi masa gaisuwa da jinjina tare da nuna masa goyon baya, kamar yadda shafin intanet na UNESCO ya bayyana.

A bisa al'ada dai, sarkin Kano na daga jagororin Musulmi mafi girma a Nijeriya bayan Sarkin Musulmi, wanda shi ne jagoran Musulmi a arewacin Nijeriya.

Sarakunan gargajiya dake da dama a Nijeriya ba su da wani aiki a kundin tsarin mulkin ƙasar, amma suna da muhimmanci wajen alkinta al'adu, abin da ya sa suke da matuƙar tasiri a ƙasar mafi yawan jama'a a Afirka.

A watan Yunin bana, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta hana hawan babbar sallah saboda fargabar fuskanatar matsalar tsaro, bayan hankula suna tashi sakamakon ɓangarori biyu sun yi iƙirarin halascin sarautar birnin mai tarihi.

'samar da ayyukan yi'

Wata "masana'anta ce da ke samar da ayyukan yi, da bunƙasa tattalin rzikin jama'a da dama," a cewar Hajo Sani.

Bikin ya "bunƙasa inda ya zama fitacce har ma ya zama birane da dama a arewacin Nijeriya har da Abuja na gudanar da shi," a cewarta.

Hawan na sallah ya shiga cikin manyan bukukuwan al'ada na Nijeriya da ke jerin bukuwan al'ada na UNESCO, da suka haɗa da bikin al'ada na Sukur da ake gudanarwa jihar Adamawa kusa da kan iyakar Nijeriya da Kamaru, da kuma bikin sacred grove mai tsarki na Osogbo a jihar Osun.

TRT Afrika