Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya WFP ya bayyana cewa ana bukatar dala miliyan 140 domin kai agaji ga ‘yan gudun hijira a Chadi tsawon wata shida.
Daraktan shirin na WFP a Chadi, Pierre Honnorat, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a yayin taron manema labarai.
Ya bayyana damuwarsa kan halin da ake ciki na rashin kudi.
Jami'in ya kara da cewa Chadi na zagaye da kasashen da ke fuskantar rikici kuma kasar ta karbi bakuncin ‘yan gudun hijira kimanin 600,000 daga Sudan da Nijar da Kamaru da kuma Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka.
Honnorat ya bayyana cewa a 2022, kashi 90 cikin 100 na ‘yan gudun hijira sun kasance cikin bukatar taimako, wanda hakan ya sa aka samu karuwar masu fama da yunwa da karin rikici a sansanoni da kuma rashin lafiya.
Ya bayyana cewa 2023 “ta kasance wata shekara da aka wahala sakamakon babu kudaden da za a taimaka wa ‘yan gudun hijira da wadanda suka rasa muhallansu daga watan Mayu zuwa sama,” in ji Honnorat.
Ya kuma bayyana cewa WFP na da burin tallafa wa akalla kashi 30 cikin 100 na masu tsananin bukata. Honnorat ya ce gwamnatin Chadi na bukatar agajin kasa da kasa ta hanyar karbar ‘yan gudun hijira musamman kafin lokacin da za a yi girbi a gonaki.
A lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, ya ce alkaluma sun nuna cewa akwai sama da mutum miliyan biyu a Chadi wadanda ke fama da karancin abinci a 2022.
“Akwai bukatar duka ‘yan gudun hijira 600,000 a tallafa musu; za a iya misali ba su fulotai domin su dogara da kansu,” kamar yadda ya kara da cewa.
Matthew Saltmarsh daga hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ya ce hukumarsa na kokarin samun dala miliyan 172.5 a bana domin tallafa wa mutum miliyan daya wadanda aka tilasta musu barin muhallansu a Chadi.