Wani harin sama da aka kai wani ƙauye a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya ya kashe aƙalla mutum 33 a makon da ya wuce, kamar yadda wasu mutum huɗu mazauna garin da kuma wani basarake a yankin suka faɗa, bayan wani farmaki da sojoji suka yi nufin kai wa maɓoyar gungun masu satar mutane.
Lamarin ya faru ne ranar 10 ga watan Afrilu, a wani harin sama mafi muni na baya-bayan nan na sojoji da ya ƙare a kan fararen hula.
A ranar Alhamis rundunar soji ta ce sojojin suka kai farmakin inda suka kawar da wasu gungun ‘yan bindiga a wasu wurare a Zamfara ciki har da karamar hukumar Maradun.
Amma Lawali Ango, maigarin ƙauyen Dogon Daji da ke Maradun, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa babu ‘yan fashi a yankinsa.
Ƙarar fashewa
Ango ya ce ya yi nisa da ƙauyen nasu a ranar 10 ga watan Afrilu, yana shirye-shiryen gudanar da bikin ƙaramar sallar da misalin karfe 0700 agogon GMT, sai ya ga jirgi na wucewa. Bayan haka ne sai ya ji fashewar bama-bamai masu ƙarfi.
A lokacin da ya yi ƙoƙarin tuntuɓar ƙauyen nasu, sai kiran ya ƙi shiga, nan da nan sai shi da sauran mutanen da siuke tare suka yi gaggawar komawa gida a baburansu.
“Da muka isa wajen, sai muka ga yara da maza da mata ... sun mutu kuma sun maƙale a cikin gine-ginen da suka rushe wanda bam ya rusa,” kamar yadda Ango ya faɗa ta wayar tarho, yana mai cewa mutum 33 ne suka mutu.
“Su sojojin suna cewa ƴan bindigar sun tsere ne suka nemi wajen fakewa a ƙauyenmu. Na rantse ba haka ba ne, zan iya zuwa ko ina a duniya na tabbatar da hakan.”
Tattara bayanan sirri cikin tsantseni
Mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta Nijeriya Manjo Janar Edward Buba ya ƙaryata cewa an kashe fararen hula a hare-harenm saboda sai da aka tattara bayanan sirri cikin nutsuwa kafin a kai harin.
“Don haka, an kai hare-haren ne kan ‘yan ta’adda ba fararen hula ba,” in ji Buba, a wani sakon tes da ya aike. Bai bayar da adadin wadanda suka mutu ba.
A watan Disambar da ya gabata, wani harin jiragen yaƙi mara matuki na soja ya kashe aƙalla mutum 85 a arewacin Kaduna, lamarin da rundunar ta ce za ta gudanar da bincike.
A watan Janairu ne dai rundunar sojin saman Nijeriya ta amince a karon farko daɗaukar alhakin harin da aka kai ta sama wanda ya hallaka fararen hula da dama shekara guda da ta wuce.
Bayan yankin da ake yaki a yankin arewa maso gabas, an yi kira ga sojoji da su tunkari barazanar da ke ci gaba da tabarbarewa a yankin arewa maso yammacin Nijeriya da kuma yankin tsakiyar ƙasar da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke kai hare-hare da kuma yin garkuwa da jama’a.