Macron ya jinjina wa jakadun kasar bisa zage dantse kan ayyukansu. / Hoto: AA

Har yanzu jakadan Faransa a Jamhuriyar Nijar bai fita daga kasar ba duk da wa'adin da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar suka ba shi na barin kasar, a cewar shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Marcon ya bayyana haka ne ranar Litinin.

A yayin da yake jawabi game da shirye-shiryen Faransa kan kasashen waje a birnin Paris, Macron ya tabbatar da cewa jakadan kasar Sylvain Itte yana a Yamai duk da wa'adin awa 48 da sojoji suka ba shi ya fita daga kasar.

"Faransa da ma'aikatan diflomasiyyarta sun fuskanci irin wannan kalubale a wasu kasashe a watannin baya-bayan nan, daga Sudan, inda Faransa ta zama abar misali, zuwa Nijar, inda abu yake faruwa a yanzu kuma ina jinjina wa abokan aikinku wadanda suke zaune a wuraren da suke aiki," in ji sanarwar.

Ranar 26 ga watan Yuli aka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum sannan aka tsare shi da iyalinsa a juyin mulkin da Faransa Faransa da wasu kasashe suka yi Allah wadai da shi.

Ranar Juma'a, ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta fitar da sanarwar bai wa jakadan Faransa wa'adin awa 48 ya fice daga kasar, tana zarginsa da kin amsa gayyatar kasar da kuma yin abubuwan da "suka saba wa muradun Nijar".

Macron ya dage cewa Faransa ba za ta sauya matsayinta game da juyin mulkin da aka yi a Nijar ba sannan ya ce zai taimaka wa Bazoum, yana mai cewa an zabe shi a turbar dimokuradiyya kuma ya yi "kyauta" da ya ki yin murabus

"Tsarinmu a fayyace yake: ba ma goyon bayan masu juyin mulki," in ji Macron.

AFP