Ali Bongo ya ce an raba shi da iyalansa inda aka tsare shi a cikin gidansa shi kada./Hoto: AA

Sojan da ya jagoranci yi wa shugaban Gabon Ali Bongo juyin mulki ya ce hambararren shugaban yana da damar fita daga kasar duk lokacin da yake so.

Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya bayyana haka a wani sako da aka karanta a gidan talabijin na kasar ranar Laraba, ya ce Bongo "yana da 'yancin yin tafiye-tafiye... kuma yana iya yin tafiya kasashen waje a duk lokacin da ya so yin hakan."

An yi wa Bongo, wanda ya shafe shekara 14 a kan mulki, daurin-talala tun ranar 30 ga watan Agusta lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatinsa ba tare da zubar da jini ba, kasa da awa daya bayan an ayyana shi a matsayin mutumin da ya lashe zaben shugaban kasar karo na uku.

Labari mai alaka: Tarihin Ali Bongo Ondimba

"Idan aka yi la'akari da yanayin lafiyar tsohon shugaban kasa Ali Bongo Ondimba, an san ya kamata ya samu 'yancin tafiya inda yake so. Yana iya tafiya kasashen waje domin a duba lafiyarsa idan yana so," in ji wata sanara da Kanar Ulrich Manfoumbi Manfoumbi ya karanta, wadda Nguema ya saka wa hannu.

Ranar Litinin aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar.

Bongo ya yi fama da larurar shanyewar barin jiki mai tsanani a watan Oktoba na 2018 wadda ta hana shi walwala, musamman yadda yake shan wahalar motsa kafarsa da hannunsa na dama.

TRT Afrika