Kamun da aka yi wa shugaban na NLC na zuwa ne kwanaki bayan ya amsa goron gayyatar ‘yan sanda a ranar 28 ga Agusta. / Hoto: Others

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya NLC ta sanar da cewa hukumar tsaro ta DSS ta cafke shugaban NLC Joe Ajaero.

Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet a ranar Litinin.

NLC ɗin ta ce an kama Ajaero a filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Litinin a lokacin da yake hanyarsa ta zuwa Birtaniya bayan ƙungiyar ƙwadago ta Birtaniya ta gayyace shi domin halartar wani taro, kamar yadda sanarwar ƙungiyar ta bayyana.

“Muna so mu bayyana ƙarara cewa an tsare Comrade Ajaero ba tare da wata takardar sammaci ko bin tsarin shari’a ba. Joe Ajaero ba mai gudun hijira ba ne. Don haka tsare shi rashin bin doka da oda da baraza ne domin babu wata hukuma da ta tabbatar da cewa tana neman sa,” in ji sanarwar ta NLC.

Kamun da aka yi wa shugaban na NLC na zuwa ne kwanaki bayan ya amsa goron gayyatar ‘yan sanda a ranar 28 ga Agusta.

Sai dai ‘yan sandan sun sake shi kwana guda bayan hakan.

TRT Afrika