Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta soke matsayin ɗan ƙasa na wasu makusantan hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
Mutanen da lamarin ya shafa sun haɗa da tsohon minista a fadar shugaban ƙasa, Rhissa Ag Boula, wanda a halin yanzu yake gudun hijira a Faransa. Sauran mutanen takwas su ma suna zaune a ƙasashen ƙetare, a cewar kafar watsa labarai ta ActuNiger.
An "soke matsayinsu na kasance 'yan ƙasar Nijar saboda aikata manyan laifuka da ke barazana ga tsaron ƙasa," a cewar wata sanarwa da shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Abdourahamane Tiani.
Sanarwar ta ce "za a hukunta mutanen da ke da hannu wajen ayyukan ta'addanci da cin amanar ƙasa da yin leƙen asiri ga ƙasashen waje masu ƙarfin iko."
Hukumomi sun ƙarfafa matakan tsaro domin "matsayin ƙasar tare da tabbatar da doka da oda," in ji sanarwar.
Mutanen da ake zargi suna aikata laifuka tare da tunzura jama'a su yi "ayyukan da za su jefa ƙasa cikin rikici".
"Waɗannan laifuka sun haɗa da haɗa baki da ƙasashen waje da leƙen asiri da cin amanar ƙasa da kashe gwiwar sojojin ƙasa."
Sojojin Nijar sun kifar da gwamnatin zaɓaɓɓen Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023, wanda suke tsare da shi tun daga wancan lokacin.