Sojojin da ke mulki a Mali sun fitar da wata doka wadda za ta kafa kwamitin da zai shirya tattaunawar sulhu da zaman lafiya a kasar, bayan da ta kawo karshen yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da 'yan tawayen Azbinawa a shekarar 2015.
Shawarar kawo karshen abin da ake kira yarjejeniyar Algiers na dada fargabar tabarbarewar rashin tsaro a kasar da ke yammacin Afirka.
A wani yunkuri na kafa sabon tsarin zaman lafiya na cikin gida, dokar ta gwamnatin mulkin soja ta bayyana tsarin kwamitin da kuma matakan da ya kamata ta dauka na shirya tattaunawa.
Ba ta bada wani lokaci ba ko kuma bayyana kungiyoyin da take son sakawa a cikin tattaunawar ba.
Mai magana da yawun ƴan tawayen na Azbinawa Mohamed Elmaouloud Ramadane a ranar Asabar ya bayyana shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wannan tsarin shiri ne na musamman tsakanin kungiyoyin da suka hada kansu.
Yarjejeniyar da aka soke
Gamayyar kungiyoyin 'yan tawayen Azbinawa a ranar Juma'a ta tabbatar da kawo karshen yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a shekarar 2015 a wata sanarwa da ta fitar tare da yin kira ga mambobinsu da su sake nazari tare da sabunta manufofinsu dangane da sabon halin da ake ciki.
Mali na fama da rikici tun daga 2012 bayan da wasu ƴan bindiga suka ƙwace iko da rikicin da ƴan tawayen Tuareg suke yi waɗanda a lokacin suke ƙorafi kan yadda gwamnatin ƙasar ta yi watsi da su, inda suke son kafa wani yanki nasu mai suna Azawad.
Azbinawan sun saka hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin Bamako a 2015, sai dai ƙungiyoyin ƴan bindiga sun kashe dubban farar hula a yaƙe-yaƙen da suka bazu zuwa Burkina Faso da Nijar masu makwaftaka.
Fatattakar dakarun kasashen waje
Yarjejeniyar ta Azbinawa ta shiga wani hali tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki sau biyu a kasar, a shekarar 2020 da kuma 2021.
Sojojin sun kori dakarun Faransa da kuma na wanzanar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke aiki a ƙasar.
Rikici tsakanin sojojin Mali da ƴan awaren ya ƙaru matuƙa tun daga Agustan bara tun bayan da sojojin wanzar da zaman lafiya suka soma janyewa.