Gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta ce ta fara samun rahotanni kan sace dalibai 10 da aka yi a karamar hukumar Kachia.
An sace daliban ne daga makarantar sakandaren gwamnati ta je-ka-ka-dawo da ke Awon a ranar Litinin, a cewar sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Tsaro ta fitar ranar Talata.
“Har yanzu ba a gano takamaimai wajen da lamarin ya faru ba, amma cikakkun rahotannin da ake jira za su fayyace kan ko a cikin harabar makarantar aka sace daliban ko kuma a wani wajen daban,” in ji sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishin ma’aikatar, Samuel Aruwan.
Kazalika gwamnatin ta ce za ta fitar da sanarwa ga al’umma idan ta samu karin bayanai kan lamarin.
Ko a ranar Lahadi ma sai da aka yi wani rikici a karamar hukumar Chikun da ya jawo asarar rayuka biyu da jikkata mutum shida.
Lamarin da ya kai har gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita tare da haramta wasu harkoki da suka hada da gala da farauta.
Satar mutane don karbar kudin fansa musamman ta dalibai a makarantu abu ne da ya dade yana faruwa a Nijeriya, kuma jihar Kaduna na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar.
Sai dai a baya-bayan nan lanmarin ya dan yi sauki, kuma hukumomi suna fadar irin nasarorin da suke samu wajen dakile lamarin.