Gwamnan Jihar Kano da ke Nijeriya ya ba da umarnin kama Alhaji Aminu Ado Bayero saboda zargin yunƙurin tayar da tarzoma a jihar bayan sanar da sauke shi daga sarautar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin ne raanar Asabar da safe ta hannun daraktansa na yaɗa labarai Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Abba Kabir ya ce Aminu Ado "ya shiga Kano cikin daren da ya gabata, don shiga fadar Kano da ƙarfin tsiya kwana biyu bayan sauke shi daga sarauta."
"Bisa haka ne gwamnan ya ba da umarnin kama tuɓaɓɓen Sarkin nan-take saboda kawo tsaiko a zaman lafiyar al'umma da kuma yunƙurin rusa kwanciyar hankalin da ake da shi a Kano," a cewar sanarwar.
Ranar Juma'a da tsakiyar dare ne Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu da ke Kano, daga nan ya zarce Gidan Sarki na Nasarawa, wanda ke da nisan kimanin kilomita ɗaya daga Gidan Gwamnatin Jihar Kano.
'Za mu zauna a fadar Kano har sai abin da hali ya yi'
A ranar Juma'a ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bai wa Muhammadu Sanusi II takardar kama aiki a matsayin sabon Sarki, kwana ɗaya bayan sa hannu a gyaran dokar Masaratun Kano ta 2024, wacce ta rushe masarautun jihar biyar ta kuma sauke sarakunan jihar, kamar yadda gwamnan ya ce.
A jawabin da ya gabatar ranar Juma'a lokacin miƙa wa Muhammadu Sanusi II takardar a fadar Gwamnatin Kano, Gwamna Abba ya ce Sarki Sanusi zai ci gaba da zama a masaukinsa ana ci gaba da al'umuran sarauta, har zuwa wani lokaci.
Sai dai ranar Juma'a da tsakar dare Sarki Sanusi II ya shiga fadar ta Kano bisa rakiyar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa da shugaban majalisa da wasu ƙusoshin gwamnati.
Matakin ya biyo bayan raɗe-raɗin cewa Alhaji Aminu Ado Bayero yana shirin komawa Kano sannan ya shiga Gidan Sarauta, kamar yadda Mataimakin Gwamnan Jihar Kwamared Aminu Abdussalam ya sanar da safiyar Asabar.
Ya yi gargaɗin cewa za su ɗauki duk wani mataki na ganin cewa naɗin da aka yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II ya tabbata.
Mataimakin gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake zanta wa da 'yan jarida da safiyar Asabar a fadar Masarautar Kano.
Ya zargi wasu da ke kusa da gwamnatin tarayya da yin amfani da jami'an tsaro wajen "ganin cewa an tanƙwara an banƙara a kan buƙatar al'ummar jihar Kano an kawo musu abin da ba shi suke buƙata ba."
"Wannan shi ne abin da ya kawo mu yau."
"Sabon Sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi ya karɓi takardarsa ta kama aiki, kuma muna kawo shi nan gidan, muna zagaya gidan da shi," kamar yadda ya shaida wa 'yan jarida a fadar Sarkin Kano.
Ya ƙara da cewa duk wasu manya na gwamnati Kano suna fadar Sarki, kuma za su kasance a fadar har sai komai ya daidaita.
"Gwamna ne ma gaba ɗaya da gwamnati muka zo muka rako Mai Martaba Sarki da shugaban majalisar da 'yan majalisa," in ji shi.
Ya zargi waɗanda suke son mayar da Sarki Aminu da yunƙurin dagula al'amura a Kano.
"Mun kasa gane me ake so a yi... a ɓata duk abin da za a ɓata... saboda ba jihar su ba ce?
Sai dai har kawo yanzu babu wani martani daga gwamnatin tarayyar ƙasar kan abin da ke faruwa a Kano da kuma zarge-zargen gwamnatin ta Kano.