Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, Abba Kabir Yusuf ya rusa kwamitocin riƙo na ƙananan hukumomin jihar 44, kamar yadda wata sanarwa da kakakin gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Laraba.
Gwamanan ya ɗauki matakin ne wanda ya fara aiki nan take, lokacin taron ban-kwana da shugabannin na riƙo da aka yi a fadar gwamnatin Kano.
Sanarwar ta ce an rushe kwamitocin riƙon ne bayan sun cika wa'adin watanni shida da gwamnan ya ba su.
Abba Kabir ya yaba wa shugabannin da aka sauke, yana mai cewa jajiricewarsu ta taimaka wajen taimakon gwamnatin gudanar da kyawawan manufofi.
Gwamnan ya umarci shugabannin da aka sauke su miƙa ragamar tafiyar da al'amura ga daraktocin mulki na kananan hukumomin, har zuwa lokacin da za a zaɓi sababbin shugabanni.
Halaccin shugabannin riƙo
A ranar 26 ga watan Oktoba ne hukumar zaben jihar mai zaman kanta za ta gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar 44, kamar yadda hukumar ta sanar.
Jihar Kano da sauran mafi yawan jihohin ƙasar dai ba su da zaɓaɓɓun shugabanni a matakan ƙananan hukumomi, inda shugabannin riƙo suke jagorantar matakin na gwamnati, wanda ya fi kusa da jama'a.
A watan Yulin 2024 ne Kotun Kolin Nijeriya ta yanke hukuncin cewa naɗa shugabannin riƙo ga ƙananan hukumomi ya saɓa wa doka.
Daga nan ne jihohin ƙasar da dama suka sanar da lokacin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.