Tun bayan mutuwar mawakin aka yi ta ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta. Hoto/Mohbad

Gwamnan Jihar Legas da ke Nijeriya Babajide Sanwo-Olu ya gayyaci jami’an DSS domin su yi bincike kan mutuwar mawakin nan Ilerioluwa Aloba wanda aka fi sani da Mohbad.

A wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Legas Gbenga Omotoso ya fitar a ranar Talata, ya ce an gayyaci jami’an na DSS ne domin su fadada binciken da ‘yan sandan Nijeriya suka faro tun bayan mutuwar mawakin mazaunin Legas.

“Mista Sanwo-Olu na umartar a gudanar da bincike domin duka wadanda ake zargi da taka wata rawa wurin mutuwar Mohbad su fuskanci shari'a.

“Saboda haka ita ma DSS ta shiga wannan binciken domin yin adalci ga matashin, iyalansa da mabiyansa,” kamar yadda ya kara da cewa.

Mohbad wanda a baya ya kasance mawaki a karkashin Naira Marley a kamfanin Marlian Records ya rasu ne a ranar 12 ga watan Satumba yana da shekara 27.

Gwamnatin ta Legas ta jajanta wa iyalan Mohbad da mabiyan Marlian Record.

Gwamnatin Legas ta bukaci duka wadanda suke da wasu bayanai da za su taimaka wa wannan binciken su bayar da su.

An gudanar da zanga-zanga kan mutuwar Mohbad a birnin Legas da Abeokuta da wasu wurare inda masu zanga-zangar ke neman a bi wa marigayin hakkinsa.

TRT Afrika