Kungiyar raya tattalin arziki kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta ce shirin da sojojin juyin mulkin Nijar ke yi na gurfanar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ba komai ba ne illa takalar fada.
Sojojin juyin mulkin na zargin Bazoum da cin amanar kasa da kuma yi wa tsaron Nijar yankan-baya.
Idan har aka gurfanar da shi aka kuma same shi da laifi, to Bazoum ka iya fuskantar hukuncin kisa, kamar yadda dokar kundin penal code ta kasar ta tsara.
Tun da fari dai sojojin Nijar sun yi ikirarin cewa Bazoum yana magana da shugabannin kasashen waje, wadanda ke fada da gwamnatin sojin tare da sanya musu takunkumai.
A wata sanarwa, ECOWAS ta ce "ta fahimci cewa ana kokarin yin wani rashin hankali na tuhumar Mohamed Bazoum da cin amanar kasa."
'Tsokanar fada'
ECOWAS ta kara da cewa ta yi "tur da wannan yunkuri saboda takalar fada ne kuma ya yi hannun riga da bayanan da hukumomin sojin suka bayar cewa za su dawo kan turbar dokar kasa ta hanyoyin lumana."
A sanarwar tata ta ranar Litinin, ECOWA ta jaddada cewa "har yanzu Bazoum ne zababben shugaban Jamhuriyar Nijar da ECOWAS ta kasashen duniya suka yarda da shi."
Labari mai alaka: Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar 'sun ki' sakin iyalan Bazoum
“ECOWAS ta yi Allah-wadai da tsare shi da ake yi ba bisa ka'ida ba, tare da kira da a sake shi ba tare da bata lokaci ba," in ji kungiyar.
Dama tun da fari Abdourahamane Tchiani wanda ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban Nijar din ya bayyana cewa juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yuli abu ne da aka yi da niyya saboda kare kasar daga rushewa da take dab da yi.
Wani mai magana da yawun rundunar sojin Nijar Kanal Manjo Amadou Abdramane, ya ce akwai isassun hujjojin tuhumar Bazoum da cin amanar kasa.
Sai dai sojojin sun ce a shirye suke su gana da jami'an ECOWAS don samo mafita ta lumana kan rikicin shugabancin na Nijar.
Baya ga takunkuman da ta saka, ECOWAS ta kuma ce a shirye dakarunta suke don yakar hambarar da Bazoum daga mulki.