Gwamnatin Ghana ta yi alkawarin karin kudi ga bangaren ciyarwa na fursunonin kasar bayan da hukumomin fursunan suka bayyana cewa suna fuskantar kalubale wurin ciyar da fursunoni.
Gwamnatin Ghana ta ce tana kashe akalla Cedi 1.80 domin ciyar da kowane fursuna daya a kullum, kamar yadda Isaac Kofi Egyir ya bayyana, Darakta Janar na Hukumar Fursunonin Ghana ya shaida wa wani kwamitin kudi na majalisar kasar a Accra a ranar Juma’a.
Zuwa watan Mayun 2022, gidajen yari a kasar da ke Yammacin Afirka na da kusan fursunoni 14,097 inda adadin fursunonin da gidajen yarin kasar ya kamata a ce sun dauka bai wuce 9,945 ba, kamar yadda hukumar gidajen yari ta Ghana ta bayyana.
A ranar Juma’a, ‘yan majalisar Ghana sun bayyana cewa suna mamakin yadda hukumar gidajen yari ta Ghana ke kokarin ciyar da kowane fursuna kan Cedi 1.80, kwatankwacin dala 0.16.
Cunkoson gidajen yari
Egyir ya bayyana cewa hukumar gidajen yari ta kasar tana da gonaki wadanda suke taimakawa wurin cike gibin abincin da ake saye na fursunonin da kudin gwamnati.
“Muna da gonaki a fadin kasar. Gonakinmu ne suke ta taimako tun bayan da aka soma samun matsalolin ciyarwa. Wannan shi ne abin da muke yi domin cike gibin kokarin da gwamnati take yi na ciyar da fursunoni,” in ji Egyir.
Mataimakin Ministan Harkokin Cikin Gida Naana Eyiah ya bayyana cewa gwamnatin kasar za ta kara adadin kudin da take bayarwa na ciyar da kowane fursuna, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito.