An tattara gawarwaki a babban birnin Sudan saboda yakin da ake yi. / Hoto: AFP Archive

A yayin da ake tsaka da fafata rikici tsakanin sojojin Sudan da dakarun Rapid Response Force (RSF), jama'a da ma'aikatan lafiya na bayyana cewa gawarwakin mutane na rubewa a kan titunan Khartoum babban birnin kasar.

Tarin gawarwaki ne da babu wanda ya taba tunanin za a same su: Da sanyin safiya aka saka gangar jikin Sadiq Abbas a wani rami mara zurfi da aka haka cikin sauri a Khartoum.

Hatta iyalai da makota da suka samu damar halartar jana'izarsa sai da suka girgiza, suna zagaya makabartar tare da yin gargadi kan hatsarin da ke tafe, in ji makocin mamacin Awad Al-Zubeer.

Hamdala kan yadda babu wanda ya zo

Kusan watanni hudu, ana ci gaba da fafata rikici a birnin Khartoum na Sudan, tsakanin sojojin Sudan da mayakan RSF.

Wannan rikici ya tagayyara rayuwar yau da kullum, ta yadda halartar jana'iza ma ke shan wahala.

Rikicin ya janyo an shiga mummunan yanayi, inda ake barin gawarwakin mutane su rube a kan titunan babban birnin, a yayin da rikicin ke ci gaba, kuma babu alamun sasantawa.

"Duba da wannan yanayi, idan ka tambaye ni a ina aka binne shi ba zan iya fada maka ba," in ji Al-Zubeer.

Babu wasu cikakkun alkaluma game da adadin mutanen da aka kashe a Sudan.

Ministan lafiya na kasar, Haitham Mohammed Ibrahim ya ce a watan Yuni rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 3,000, amma babu wasu karin alkaluma da aka bayyana bayan wannan.

Adadi na gaskiya na iya fin haka sosai, in ji likitoci da masu fafutuka na kasar. Kamar yadda babu wasu likitoci da suka bayyana yawan gawarwakin da ba a iya binnewa ba, musamman yadda ake ganin kaburbura manya a yankin Darfur na kudancin kasar da ke fama da kashe-kashen kabilanci.

Mutuwa saboda yunwa

An kashe mafi yawan fararen-hula da suka fito daga babban birnin Sudan a yayin musayar wuta, inda garin mai nutsuwa ya koma filin daga, in ji kungiyar likitocin kasar.

Wasu kuma sun mutu saboda yunwa, sakamakon yadda ba sa iya fita waje yayin da ake musayar wuta.

A lokacin da gari ke zaune lafiya, ana halartar jana'iza sosai a Sudan, ana zaman makoki tsawon kwanaki, kuma dubban mutane na halarta.

A al'adar mutanen Sudan ana wankewa tare da yin addu'o'i ga mamaci kafin makusantansa su saka shi a kabari.

A ra'ayin wasu mutane bakwai da suke rayuwa a Khartoum ko suka taba rayuwa a can, wannan yaki da bangaren shugabanni biyu ke fafatawa a kasar, shugaban sojoji Janaral Abdel Fattah Al Burhan da kwamandan RSF Mohammed Hamdan Dagalo, ya lalata wannan al'ada.

Wasu mutanen uku sun bayyana ra'ayinsu amma sun nemi a boye sunansu saboda yiwuwar ramuwar gayya.

Mutane da dama sun bayyana cewa abu ne mai wahala a iya zuwa manyan makabartu biyu da ke babban birnin, a yayin da suke son binne 'yan uwa, abokan arziki ko wadanda yakin ya rutsa da su.

Rikici ya rutsa da su a Jami'ar Khartoum

Sama da dalibai 100 ne rikici ya rutsa da su a Jami'ar Khartoum a ranar 15 ga Afrilu.

Khaled, dalibin da aka harba a kirji ya mutu jim kadan bayan harsashi ya same shi, in ji wani dalibi.

"Mun janyo gawarsa zuwa kusa da gida don hana ta rubewa," in ji shi, amma ya nemi a boye sunansa gudun kar a kai masa hari shi ma.

Tare da sauran abokansa suka lullube Khaled, suka binne shi a filin jami'ar a karkashin wata bishiya bayan samun izini daga makarantar.

Gasin Amin Oshi, wani mazaunin yankin Bayt Al-Mal da ke Omdurman, wanda ke daura da kogin Nil daga Khortoum, ya bayyana cewa dakarun RSF sun hana wasu makotansu binne 'yar uwarsu da ta mutu a wata makabarta da ke kusa da su.

Sun binne matar, wadda ta mutu sakamakon rashin lafiya a filin wata makaranta.

Mafi yawan mazaunan sun bayyana cewa dakarun RSF da suke rike da iko da mafi yawan birnin, suna yawan janyo takura da tarwatsa jama'a.

A kwanakin farko na rikicin, sojoji sun kai wa sansanonin RSF harin bama-bamai da ke babban birnin, wanda hakan ya sanya RSF ba su da matsuguni sai suka karbe gidajen jama'a suka mayar da su sansanoninsu.

Su kuma sojojin sai suka fara kai wa gidajen fararen hula hari ta sama da bama-bamai. Sama da mutum miliyan 2.15 sun bar birni Khartoum, kamar yadda alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana.

El-Zubeer ya bayyana cewa makocinsa Abbas, ya gamu da harbin bindiga bayan da RSF suka kai samame gidansa tare da gano daya daga cikin 'yan uwansa soja ne, dayan kuma jami'in leken asiri.

Bayan an kai gawar Abbas asibiti, sai mayakan na RSF suka hana a binne shi ba tare da bayar da wani dalili ba, amma daga baya suka ji rokon iyalinsa.

Mafi yawan mutane sun ji tsoron halartar jana'izar ta ranar 30 ga Yuni, ko kuma ba su san da ita ba, in ji El-Zubeer.

Tun bayan fara rikicin kasar ke fuskantar daukewar lantarki da katsewar yanar gizo.

El-Zubeer ya kara da cewa "Wayoyin hannu na da amfani irin na kwalayen taba sigari."

Kakakin shugaban RSF, Youssef Izzat ya bayyana cewa shugabancinsu bai bayar da umarnin hana fararen hula binne mamatansu ba.

An gaza binne dubban gawarwaki

Wani mazaunin kudancin birnin Khartoum ya ce duk da a baya mayakan RSF na satar kayan mutane, mayakan sun taba shirya jana'za da bayar da motar daukar gawa bayan mutuwar kawunsa a watan Yuli.

Tun watan Yuni, Kungiyar Bayar da Agaji ta Sudan na tattara gawarwaki a babban birnin Khartoum. Kungiyar ta ce ta samu damar ganowa da binne mutum 102, mafi yawansu mayaka daga dukkan bangarorin biyu.

Ana daukar hotunan gawarwakin tare da ba su lambobi, in ji wani ma'aikacin kungiyar.

Amma yadda yaki ya hana a shiga unguwanni da dama, akwai yiwuwar ba a binne dubbai ba a babban birnin, in ji Kungiyar Bayar da Agaji ta Kasa da Kasa ta Save the Children.

A watan da ya gabata, wasu mutane daga gundumar Bahri da ke arewacin birnin Khartoum sun kira likitoci don su zo su kwashe gawarwaki kusan 500 na mayakan RSF da suke rubewa a kan tituna.

A kudancin Khartoum, an kirga gawarwaki 26 mafi yawansu na mayakan RSF da fararen hula kwance a kan titunan a 'yan makonnin nan da suka wuce.

Ana kai gawarwakin da ba a iya tantance su waye ba zuwa mutuware, amma rikicin ya janyo barin irin wadannan wurare har guda hudu da ke birnin.

TRT World