Daga Melike Yazir Gocer
Yadda dazuka suka mamaye kaso 88 na kasarta, Gabon ta karbi dala miliyan 17 da Asusun Dazukan Tsakiyar Afirka (CAFI), shirin da Majalisar Dinkin Duniya take daukar nauyi, saboda gudunmowar da kasar ke bayarwa wajen zuke iskar carbon a duniya ta hanyar dazukanta da take adanawa.
Saboda nuna godiya ga wadannan ayyuka ne ya sanya aka zabi Babban Birnin Gabon don karbar bakuncin taron “Makon Yanayi na Afirka” da aka gudanar a tsakanin 29 ga Agusta da 2 ga Satumba.
A wannan kokari, an yi tattaunawa tsakanin kungiyoyin fararen hula da shugabanni domin samun damar bayyana matsayin Afirka kan COP27, da za a yi a watan Nuwamba.
Damar tattalin arziki ta dala biliyan biyu
Kowa ya yabawa Gabon saboda rawar da take takawa da zama zakaran gwajin dafi wajen kare dazukanta da korran bishiyu, da kuma yaki da dumamar yanayi.
Daya daga cikin kasashe kadan a duniya ne da tattalin arzikinsu yake tabuwa saboda iskar carbon.
Kasar na zuke tan miliyan 140 na iskar carbon daga ban kasa inda take fitar da tan miliyan 40 kawai.
A wajen gwamnatin Gabon, dole ne manyan masu grubata muhalli su dauki nauyin ayyukan dasa bishiyu da adana dazuzzuka.
Godiya ga ayyukan hana yaduwar carbon da take yi, “Huhuwan duniya na biyu” na son a saka mata saboda nasarar da ta yi wajen karewa da tsare muhalli, maimakon sare bishiyun don samar da katako, da samar da manja, wanda sh, ne abun da wasu kasashen Afirka da dama suke yi.
Lee White, masanin kimiyyar kasa kuma Ministan Ruwa, gandun daji da harkokin teku na Gabon ya bayyana cewa, kasarsa na son ribatar dorewar dazukanta don ta samu kudaden shiga.
Asusun carbon
Asusu kan iskar cabon na wakiltar babbar dama ga Gabon, kuma ta samu wannan yabo ne sakamakon “Rage Fitar da Gurbatacciyar Iskar Carbon da Hana Dazuka Lalacewa”, wanda aiki ne da Majalisar Dinkin Duniya ke goyon baya karkashin Yaki da Sauyin Yanayi.
Madalla ga wannan kasuwa, wadda aka kebewa kasashe da kamfanunnuka, asusu kan carbon zai zama masamar kudade sama da yadda ake samun su ga sare dazuka.
A Turai, dole ne kasashe su bi ka’idar fitar da iskar carbon; misali a Faransa, ba a yarda a fitar da sama da tan miliyan 450 ba a 2020.
Idan kamfani ko kasa ya fitar da iskar carbon sama da yadda aka kayyade, dole ne su zuba kudi a asusun carbon don biyan diyyar fitar da ita sama da yadda aka amince su fitar.
Kamfani a Faransa zai iya fitar da carbon din da ya ga dama ta hanyar bayar da kudade ga Gabon.
Libreville na son kirkirar asusun carbon miliyn 187 --- duk asusu daya zai dauki tan miliyan 1 na carbon. Kuma za su sayar da su don samun dala biliyan 2.
Kasar na kuma kammala kafa doka da za ta kula da kudaden da ake samu daga sayar da wadannan asusu na carbon.
Ana tsammanin kaso 35 na kudin shigar da za a samu, za a sake juya shi wajen kare dazuka da ci gaba mai dorewa, kaso 15 na kudaden kuma za a kashe wajen raya karkara, inda kaso 50 kuma za a dinga biyan basussuka da cike gibin kasafin kudi.
A lokacin da ake ta muhawara game da sahihancin asusun carbon, fararen fata na kallon asusun carbon a matsayin mai matukar muhimmanci ga wanzuwar dazuka.
Kare halittun teku
Domin cimma manufar yaki da dumamar yanayi, gwamnati ta kaddamar da shirye-shirye da dama, da suka hada da samar da azuka, kare dabbobin ruwa da na daji da sauran shirye-shirye.
Tare da kirkirar wajen adana halittun teku mafi girma a Afirka, Libreville na kare halittun tekunsa da suke da yawa tare da aiwatar da kiwon kifi mai dorewa.
Ma’ajiyar halittun ruwa dake lambunan shakatawa 20 na dauke da kaso 26 na ruwan kasar Gabon, kuma ya mamayi waje mai girman sukwayamita 53,000.
Masunta ba sa samun damar amfani da dabarun kamun kifi marasa dorewa ba, sannan an hana kamun kifi gaba daya a wasu yankunan.
A lokacin da masanan kimiyya ba za su yi muhawara game da cewar kare tekuna hana halittun ruwa illata daga sauyin yanayi, suna zama cikin yanayi mai kyau, kuma sauyi mummuna ba zai shafe su ba.
Misali ba zai yiwu ka kare dabbobin waje daga zafin dake karuwa ba, amma kare su, zai rage yawan kamun kifi da gurbatar ruwan, wanda zai taimaka musu wajen murmurewa da wuri.
Misali, sama da kaso 90 na halittun dake cikin ruwan ‘Chagos Archipelago Marine’ na karkashin kariya, amma a 1998 duk sun bace saboda kodewa, amma kumaa 2010, an kare su inda suka farfado.
Kare dazuka da gwagwarmaa hana satar namun dawa
Gwamnatin Gabon ta kirkiri wuraren shakatawa na kasa guda 13 wanda sun kai girman kaso 13 na fadin kasar gabon, domin amintar da dazukansu daga mutuwa.
Daya daga abubuwan da Gabon ta mayar da hankali shi ne hana satar namun dawa musamman wadanda suke gaf da karewa.
Idan kafa filayen shakatawa 13 na bayar da damar kare dabbobi irin su giwa da birrai da gwaggon biri da tsitaka da jami’an tsaro kuma na murkushe mafarauta a dazuka dake satar dabbobin.
Ana ganin kyakkyawan sakamakon wannan mataki. A lokacin da adadin giwaye ya ragu da kaso 86 a duniya a sheksru 30 da suka gabata, a Gabon kuma adadinsu ya ninka a shekru 10 da suka gabata.
Jama’a za su san hanin da aka yi game da hana farauta, amma har yanzu ba a san yadda rayuwar mutanen da suka dogara kan noma da kuma namun dawa za ta kasance tare da su ba.
Wasu na inkarin irin tasirin da dabbobi suke da shi kan albarkatun gonarsu: Dabbobi --- giwaye, na lalata amfanin gona, kuma mazauna wadannan yankuna ba su da ‘Yancin tsoma baki ko dakatar da dabbobin.
Yadda dabbobi sukelalata abinci, mazauna yankunan na korafin ba su da damar kare dukiyoyinsu.
Abun da yake sama da komai ma, kasar na wayar da kan jama’a game da batutuwan sauyin yanayi.
Ana yin tarukan wayar da kan jama’a don bayyana musu amfanin kare dabbobi da dazuka, da kuma irin amfanin da suke da shi ga rayuwar jama’a.